KORONA: Abuja 65, Barno 42, Kano 1, Najeriya ta samu karin mutum 627 ranar Juma’a, yanzu ta zarce mutum 15,000

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 627 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Juma’a.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum Lagos-229, FCT-65, Abia-54, Borno-42, Oyo-35, Rivers-28, Edo-28, Gombe-27, Ogun-21, Plateau-18, Delta-18, Bauchi-10, Kaduna-10, Benue-9, Ondo-8, Kwara-6, Nasarawa-4, Enugu-4
Sokoto-3, Niger-3, Kebbi-3, Yobe-1, Kano-1.

Yanzu mutum 15181 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 4891 sun warke, 399 sun rasu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 6,611, sai FCT – 1,097, Kano – 1, 048, Ogun – 523, Edo – 490, Rivers – 454, Oyo – 434, Katsina – 411, Bauchi – 392, Kaduna – 239, Borno – 381, Jigawa – 314, Gombe – 293, Delta – 225, Ebonyi – 152, Kwara – 143, Plateau – 130, Sokoto – 129, Nasarawa – 128, Imo – 114, Abia – 97, Zamfara – 76, Ondo – 54, Anambra – 53, Yobe – 52, Osun – 50, Kebbi – 47, Niger – 46, Akwa Ibom – 45, Adamawa – 42, Enugu – 35, Bayelsa – 32, Ekiti – 30, Taraba – 18, Benue – 13, da Kogi – 3.

Share.

game da Author