Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 661 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Asabar.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Juma’a sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum -230, Ribas-127, Delta-83, FCT-60, Oyo-51, Edo-31, Bayelsa-27, Kaduna-25
Plateau-13, Ondo-6, Nasarawa-3, Ekiti-2
Kano-2, Borno-1.
Yanzu mutum 19,808 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 6,718 sun warke, 506 sun rasu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum, 8, 407, sai babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja dake da – 1,549, Kano – 1,184, Oyo – 860, Edo – 779, Rivers – 866, Ogun – 623, Kaduna – 552, Borno – 476, Gombe – 451, Bauchi – 447, Katsina – 426, Delta – 502, Jigawa – 317, Ebonyi – 234, Plateau – 220, Imo – 205, Nasarawa – 184, Kwara – 180, Sokoto – 135, Ondo – 134, Bayelsa – 155, Enugu – 126, Zamfara – 76, Kebbi – 67, Anambra – 66, Niger – 66, Yobe – 56, Osun – 54, Akwa Ibom – 65, Adamawa – 42, Benue – 39, Ekiti – 34, Taraba – 18, Taraba – 18, da Kogi – 3.
Hukumar NCDC ta gargadi mutane da su kula da tsoffi musamman wadanda ke fama da rashin lafiya kamar Asma, ciwon siga da dai sauran su. Hukumar ta ce likitoci sun shaida cewa lallai irin wadannan tsofaffi sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar.
Haka zalika, idan ba a manta ba, gwamnan Jigawa Mohammed Badaru ya shaida cewa jihar ta sallami duka wadanda suka kamu da cutar.
Gwamna Badaru ya ce mutum daya ne tal ya rage a jihar bai warke ba tukunna.