KORONA: Abu dai sai gaba-gaba ya ke, Najeriya ta samu karin mutum 681 ranar Alhamis, Yanzu mutum 14,554 suka kamu

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 681 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 345, Rivers – 51, Ogun – 48, Gombe – 47, Oyo _36, Imo-31, Delta – 28, Kano – 23, Bauchi – 18, Edo – 12, Katsina – 12, Kaduna(9), Anambra – 7, Jigawa- 5 Kebbi – 4, Ondo – 4 and Nasarawa – 1., Baylesa – 2, Kebbi – 2 and , Plateau – 2.

Yanzu mutum 14,554 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 4,494 sun warke, 387 sun rasu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 6,611, sai FCT – 1,097, Kano – 1, 048, Ogun – 523, Edo – 490, Rivers – 454, Oyo – 434, Katsina – 411, Bauchi – 392, Kaduna – 239, Borno – 381, Jigawa – 314, Gombe – 293, Delta – 225, Ebonyi – 152, Kwara – 143, Plateau – 130, Sokoto – 129, Nasarawa – 128, Imo – 114, Abia – 97, Zamfara – 76, Ondo – 54, Anambra – 53, Yobe – 52, Osun – 50, Kebbi – 47, Niger – 46, Akwa Ibom – 45, Adamawa – 42, Enugu – 35, Bayelsa – 32, Ekiti – 30, Taraba – 18, Benue – 13, da Kogi – 3.

Share.

game da Author