KOMAWAR OBASEKI PDP: Lokacin da Oshiomhole zai kidime ya tiki rawa tsirara a kasuwa ya zo – Saraki

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana farin cikin canjin shekar da Gwamna Godwin Obaseki na Jihar Edo ya yi, daga APC zuwa PDP.

Obaseki ya koma PDP a ranar Juma’a, bayan ya fice daga APC ranar Talata, sakamakon kin tantance shi ya sake tsayawa takara zango na biyu.

Bisa daurin gindin Adams Oshiomhole, wanda ke rigima da Obaseki, APC ta tsayar da Eze Iyamu takarar gwamna, a zaben wanda zai gudana ranar 19 Ga Satumba, 2020.

Iyamu dai a karkashin PDP ya yi takara a zaben gwamnan Edo na 2016. Yanzu kuma ta juya, ya koma APC, shi kuma Obaseki ya koma PDP.

Da ya ke karin bayani dangane da wannan dambarwa, Saraki ya ce, “Na yi biris na kauda kai Oshiomhole ya rika ci min mutunci, ya na bi na da sharri da yarfe. To yanzu lokaci ya yi da santsin siyasa zai kwashe shi ya gigice ya afka cikin kasuwa ya na tikar rawa tsirara.

“Oshiomhole da ke fankamar zai kawo karshen siyasar wani, to shi ne ma a yanzu zai gamu da gamon sa.”Inji Saraki

Ya kara da cewa Oshiomhole ya yi amfani da mugaye da bakaken kalaman bakin sa, ya lalata jam’iyyar APC.

Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya taya Obaseki murnar rabuwa da jam’iyyar da ya kira ta bankaura, ya dawo cikin jam’iyyar PDP wadda ta san mutunci da martabar dimokradiyya.

Share.

game da Author