KAURACE WA AIKI: Zulum ya dakatar da duka ma’aikatan lafiya na asibitin Ngala

0

Gwamnan Barno Babagana zulum ya dakatar da duka ma’aikatan lafiya na babban asibiti dake garin Ngala.

Hakan ya biyo bayan ziyarar bazata ne da yayi wa wannan asibiti inda ya cikaro da wani abin da ya tada masa hankali.

Isar gwamna Zulum ke da wuya wannan asibiti dake garin Ngala sai ya iske babu ma’aikacin gwamnati ko daya sai mai’aikatankungiya mai zaman kan ta ‘fhi360’ ne ke aiki a asibiti.

Sune suke duba marasa lafiya da sauran wadanda mutan gari za su dasu baya ga yan gudun hijri da suke duba wa.

Wannan abu yayi matukar tada masa da hankali.

A jawabin da yayi, Zulum ya ce ” Sannan wadannan likitoci da nas nas na gwamnati duk suna karbar albashi har da alawus ashe basu zuwa aiki.”

Ya umarci hukumar kula da ma’aikatan Lafiya ta jihar ta dakatar da albashin su duka sanna ta gudanar da bincike akwai.

” nan ba da dadewa ba zan dawo in sake duba halin da asibitin ke ci. ina fatan ba zan sake cin karo da abin da tarar a yau.” Kamar yadda gwamna zulum ya saka a shafin sa ta Tiwita.

Share.

game da Author