Kafin ‘yan bindiga su far wa Jami’in Kiwon Lafiya na Karamar Hukumar Danmusa, a ranar Litinin tsakar dare a garin ‘Yantumaki, a ranar wani al’amari ya faru da rana, a Fadar Mai Martaba Sarkin Katsina, Abdulmumin Kabir.
Hakimai ne su takwas suka yi masa takakkiya har fada, suka nuna masa tsakanin damuwa ganin yadda ‘yan bindiga ke neman su gagari jami’an tsaro a yankunan su.
Hakiman sun shaida wa Sarki cewa su takwas sun kuwa yin hijira daga garuruwan su, gudun Kasa ‘yan bindiga su ci gaba da bin su daya bayan daya su na yi musu kisan-gilla, kamar yadda suka yi wa Hakimin ‘Yantumaki makonni biyu da suka gabata.
PREMIUM TIMES HAUSA ta ji daga kwakwarar majiya, cewa hakiman da suka kai wa Sarkin Katsina wannan korafin sun hada da na Jibiya, Safana, Dandume, Sabuwa, Faskari, Kankara, Danmusa da Batsari.
Wasu jaridu ciki har da Daily Trust sun buga labarin takakkiyar hakiman takwas zuwa fadar Sarkin Katsina.
A wannan ranar ce cikin dare ‘yan bindiga suka koma ‘Yantumaki, suka yi awon-gaba da Mansir Yusuf da ‘yar sa.
An same shi har gida, kusan da gidan Hakimi, wanda suka bindige a gidan sa makonni biyu baya.
Wane Ne Mansir Yusuf: Shi ne Jami’in Kiwon Lafiya, mai kula da Shirin Fatattakar Cutar Maleria, wato ‘Roll Back Maleria Focal Officer (RBM).
Ya na da farin jini sosai, saboda aikin sa ya shafi hulda da jama’a kai-tsaye, musamman da ya ke aikin sa ya shafi raba gidan sauro, kawar da cutar zazzabin maleriya da kuma wasu cutukan da ke addabar yara kananan ‘yan wata shida da haihuwa zuwa watanni 59.
Zuwa har gida a sace Mansir, kwanaki 10 bayan kashe hakimi, ya harzuka matasan ‘Yantumaki, har suka fito suka datse hanya.
Garin ‘Yantumaki ba a kan lungu ya ke ba. Ya na kan titin zuwa Katsina daga Funtua, ko Malumfashi zuwa Katsina.
Garuruwan Kankara, Kurfi da Dutsinma duk a kan titin suke. To ganin yadda a kullum ‘yan bindiga ke kara ragargazar su, ya kara tunzura matasan har suka fara kone-kone, kuma suka hana motoci da ke shiga ko fita Katsina zuwa Abuja, Kaduna, Malumfashi, Funtuwa, Zamfara da Sakoto wucewa.
Sun kona allo mai dauke da hoton Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Masari.
Sannan kuma sun rika surfa zagi kan shugabannin da suka ce sun yi da-na-sanin zaben su, tun daga kan Masari har Buhari.
PREMIUM TIMES ta bada labarin cewa zanga-zanga ta barke a yankin Katsina, bayan ‘yan bindiga sun arce da jami’in lafiya da ‘yar sa.
Hasalallun matasa sun tare titin ‘Yanrumaki, cikin Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina, bayan mahara sun sace wani jami’in kiwon lafiya tare da ‘yar sa a garin.
Jami’in mai suna Mansir Yusuf, an yi masa takakkiya ne har gida aka arce da shi, makonni biyu bayan yin takakkiya a cikin garin aka kashe Hakimin garin.
Premium Times ta buga labarin yadda aka yi wa Hakimin kisan-gilla.
Mazauna garin Danmusa sun ce Mansur Yusuf makaucin hakimin ne.
Matasan dai sun datse titi su na zanga-zangar surfa wa Gwamnatin Jihar Katsina da ta Tarayya zagi, saboda matsalar tsaron da ta dabaibaye garin na ‘Yantumaki.
“Tun da aka kashe Hakimin har yau din nan da muke zanga-zanga, babu jami’an tsaro ko daya a garin nan.
“An kyale ‘yanbindiga su na karkashe mu saboda sun san babu wadanda za su iya hana su yin barnar da suka ga dama. To jiya ma ga shi sun dawo aun saci jami’in kiwon lafiya da ‘yar sa.”
PREMIUM TIMES ta kasa samun Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Katsina.
Makonni biyu baya wasu ‘yan bindiga suka kashe hakimi bayan sun yi wa Shugaban APC kisan-gilla a Katsina
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki, cikin Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
Sun kashe Abubakar Atiku awanni kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun yi wa Shugaban APC na Karamar Hukumar Batsari takakkiya har gida suka yi masa kisan gilla.
Lamarin ya faru da dare ranar Lahadi, inda maharan su ka shafe awa biyu a ‘Yantumaki su na fakon hakimin, wanda suka bindige yayin da ake ruwan sama, wajen 12 na dare.
Majiya ta tabbatar da cewa an harbi dogari daya ya ji ciwo. Said dai kuma an ce harsashe ne ya wuce ya same shi, ba shi aka yi saiti ba.
‘Yan bindigar dai ba su kashe kowa ba banda hakimin. Kuma suka yi tafiyar su.
Kisan hakimin ‘Yantumaki ya faru a ranar da aka bindige Shugaban APC na Karamar Hukumar Batsari, duk a cikin Jihar Katsina.
Shugaban mai suna Abdulhamid Sani, ‘yan bindiga sun yi masa kisan-gilla ne yayin da ya je kauyen su Dumburawa da niyyar sasanta batun rabon gado.
Majiya da kuma Tsaskar Labarai a Katsina sun tabbatar cewa Abdulhamid Sani ya na daga cikin masu sasantawa da ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Batsari.
“To wani dan bindiga mai suna Kwalli ya shiga gari, sai ‘yan banga suka kama shi, suka mika shi ga ‘yan sanda.
“Sai shuganan gungun su Kwalli mai suna Manu Wargaje, ya kira Abdulhamid ya ce ya na so ya sa baki a saki Kwalli.
“Abdulhamid ya ce ba zai iya ba, domin magana ta kai ga ‘yan sanda.
“To su dama su Manu da Kwalli ba su cikin gungun ‘yan bindigar da suka tuba.
“Sai suka samu wani magulmaci (infoma), suka ba shi kudi, suka ce duk ranar da Shugaban APC ya je kauyen su, ya sanar da su.
“Ranar da ya je Dumburawa batun rabon gado, sai ga Manu Wargaje shi da wasu mahara biyu a kan babura biyu. Suka samu Abdulhamid su ka ce za su tafi da shi, sai an sakar musu Kwalli, sannan su sake shi.
“Abdulhamid ya ce ba zai bi su ba. Jama’a kuwa suka kewaye su, aka yi cirko-cirko. Ganin haka, sai Manu ya dirka masa bindiga, amma ta ki tashi.
“Da su ka ga haka, sai suka kama shi, su na duka da sanda, kuma suka bankare hannayen sa, suka harbe shi a kasan hamatar sa. Nan ya fadi, daga baya ya rasu.”
Wata majiya ta tabbatar da cewa Fulanin da suka tuba, sun bi su Manu Wargaje sun kashe a cikin daji. Kuma suka kira jama’a domin a je a dauki gawarwakin su, kuma a shaida.
Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sanda na Katsina ya tabbatar da kisan Hakimi da na Shugaban APC.
Idan ba a manta ba, shekarun baya mahara sun yi wa Dagacin Birchi takakkiya har gida cikin Karamar Hukumar Kurfi, suka kashe shi.Yadda ‘yan bindiga suka kashe hakimi bayan sun yi wa Shugaban APC kisan-gilla a Katsina:
Wasu ‘yan bindiga sun kashe Hakimin ‘Yantumaki, cikin Karamar Hukumar Danmusa a Jihar Katsina.
Sun kashe Abubakar Atiku awanni kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun yi wa Shugaban APC na Karamar Hukumar Batsari takakkiya har gida suka yi masa kisan gilla.
Lamarin ya faru da dare ranar Lahadi, inda maharan su ka shafe awa biyu a ‘Yantumaki su na fakon hakimin, wanda suka bindige yayin da ake ruwan sama, wajen 12 na dare.
Majiya ta tabbatar da cewa an harbi dogari daya ya ji ciwo. Sai dai kuma an ce harsashe ne ya wuce ya same shi, ba shi aka yi saiti ba.
‘Yan bindigar dai ba su kashe kowa ba banda hakimin. Kuma suka yi tafiyar su.
Kisan hakimin ‘Yantumaki ya faru a ranar da aka bindige Shugaban APC na Karamar Hukumar Batsari, duk a cikin Jihar Katsina.
Shugaban mai suna Abdulhamid Sani, ‘yan bindiga sun yi masa kisan-gilla ne yayin da ya je kauyen su Dumburawa da niyyar sasanta batun rabon gado.
Majiya da kuma Tsaskar Labarai a Katsina sun tabbatar cewa Abdulhamid Sani ya na daga cikin masu sasantawa da ‘yan bindiga a Karamar Hukumar Batsari.
“To wani dan bindiga mai suna Kwalli ya shiga gari, sai ‘yan banga suka kama shi, suka mika shi ga ‘yan sanda.
“Sai shuganan gungun su Kwalli mai suna Manu Wargaje, ya kira Abdulhamid ya ce ya na so ya sa baki a saki Kwalli.
“Abdulhamid ya ce ba zai iya ba, domin magana ta kai ga ‘yan sanda.
“To su dama su Manu da Kwalli ba su cikin gungun ‘yan bindigar da suka tuba.
“Sai suka samu wani magulmaci (infoma), suka ba shi kudi, suka ce duk ranar da Shugaban APC ya je kauyen su, ya sanar da su.
“Ranar da ya je Dumburawa batun rabon gado, sai ga Manu Wargaje shi da wasu mahara biyu a kan babura biyu. Suka samu Abdulhamid su ka ce za su tafi da shi, sai an sakar musu Kwalli, sannan su sake shi.
“Abdulhamid ya ce ba zai bi su ba. Jama’a kuwa suka kewaye su, aka yi cirko-cirko. Ganin haka, sai Manu ya dirka masa bindiga, amma ta ki tashi.
“Da su ka ga haka, sai suka kama shi, su na duka da sanda, kuma suka bankare hannayen sa, suka harbe shi a kasan hamatar sa. Nan ya fadi, daga baya ya rasu.”
Wata majiya ta tabbatar da cewa Fulanin da suka tuba, sun bi su Manu Wargaje sun kashe a cikin daji. Kuma suka kira jama’a domin a je a dauki gawarwakin su, kuma a shaida.
Kakakin Yada Labaran ‘Yan Sanda na Katsina ya tabbatar da kisan Hakimi da na Shugaban APC.
Idan ba a manta ba, shekarun baya mahara sun yi wa Dagacin Birchi takakkiya har gida cikin Karamar Hukumar Kurfi, suka kashe shi.