Kungiyar kare hakkin wadanda aka yi wa fyade mai suna PARAA ta bayyana cewa akalla kashi 75 bisa 100 na kararrakin aikata fyade da ake kawo wa ofishin kungiyar duk malamai ne ko fastoci ke aikatawa.
Bayan haka shugaban kungiyar Foluke Daramola-Salako ta karyata cewa da ake yi wai irin kayan da mata ke sakawa wanda ke matse musu jiki na ingiza maza su yi musu fade.
Foluke ta ce babu gaskiya a cikin wannan magana, ” Idan mutane za su yi nazari mai zurfi, zasu gano cewa tabbas wannan magana ba haka ya ke ba domin a hukuma ta ba a taba kawo matsalar fyade da ya shafi ‘Yan mata haka ba, duka ba su wuce kananan yara ne da tsofaffi da ake bi har gida a danne da karfin tsiya.
Idan ba a manta ba a makon jiya wani mutum ya afka wa wata tsohuwa a gidan ta inda ya danne ta da karfin tsiya.
Allah ya yi mata gyadan dogo, bayan ta tsala ihu sai wani makwabcin ta ya kawo mata dauki, ya bugi wannan mutum a gadon baya da sanda.
Rahotan ya nuna cewa mutumin ya arce babu wando a jikin sa sannan ya manta da takalmi da tocilan sa a dakin wannan tsohuwa.