Hukumar kula da jin dadin dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta bayyana cewa mutane da da ma na rage shekarunsu na haihuwa domin su samun shiga tsarin yi wa kasa hidima yanzu.
Shugaban Hukumar Shuaibu Ibrahim ya sanar da haka bayan taro da hukumar ta yi ranar Talata.
Ibrahim ya ce mutane na rage shekaru su na haihuwa ne saboda karin alawus din da gwamnati ta yi wa masu yi wa kasa hidima.
” Matsalar da muke samu shine rage shekarun haihuwa da wasu dalibai ke yi don yin bautar kasa sannan da wadanda suke yi sau biyu ko fiye ma saboda wannan kari da aka yi.
Ibrahim ya ce Hukumar za ta hada hannu da Hukumar JAMB domin bankado masu aikata irin wannan laifi.
” Canje-Canje da shugaban Hukumar JAMB Ishaq Oloyede ya yi a JAMB ya taimaka wajen kawar da matsaloli da dama da Hukumar ke fama da su a da.
“A dalilin haka NYSC ta yarda ta hada hannu da hukumar JAMB domin gano wadanda basu yi wa kasa hidima ba.
Idan ba a manta ba a watan Janairu 2019 gwamnatin Muhammadu Buhari ta kara yawan alawus din da ake biyan masu yi wa kasa hidima daga Naira 19,800 zuwa 33,000.
Dalibai da dama sun jinjina wa gwamnati bisa wannan kokari da tayo tana mai cewa hakan ma zai taimakawa dalibai nasu yi wa kasa hidima matuka.