An kama wani mutum da ake zargin fitinannen mai fyade ne a garin Kwanar Dangora da ke cikin Karamar Hukumar Kiru, Jihar Kano.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar ta bayyana sunan Mai fyaden Zirfarahul Alfa, kamar yadda kakakin su Abdullahi Haruna ya bayyana.
An damke Alfa wanda aka fi sani da lakabin ‘Mai Skirt’, a lokacin da ya shiga wani gida tsakar dare da nufin yi wa wasu kananan yara fyade.
“Ya shiga dakin su sai ya kashe fitila. Yayin da mahaifiyar yara ta lura an kashe fitilar dakin, sai ya yi sauri ta tashi mijin ta daga barci. Shi kuma ya kwartsa ihu, kwsrton ya gudu. Amma aka fafare shi aka damke shi.”
Haruna ya ce kwarton ya furta da bakin sa cewa akalla ya yi wa mata da kananan yara fyade za su kai 40, a cikin shekara nan da ake ciki. Ciki kuwa har da tsohuwa mai shekara 80.
“Akwai wata gyatuma mai kimanin shekara 80 da na danne tsakar dare ana ruwan sama. Kuma ni da dare na ke shiga cikin gidaje ina fyade har cikin daki. Ina yi wa mata, amma har kananan yara ban bari ba.” Inji ‘Mai Skirt’ kamar yadda ya shaida wa ‘yan sanda
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano Habu Sani, ya umarci a damka bstun Mai Skirt’ a hannun sashen binciken masu yin fyade da bata kananan yara.
Da an kammala bincike za a damka shi ga alkali domin ya fuskanci hukunci.
Mai Skirt’ ya ce ranar sa ta baci yayin da aka kama shi cikin daki ya na kokarin yi wa yara fyade.
“Ni a cikin wannan shekarar na fara yin fyade. Har cikin gida kuma a cikin daki na ke shiga na yi fyade, wani lokaci ma har na yi na gama wadda na yi wa fyaden ba ta ma san na yi mata ba.” Inji shi.
Discussion about this post