A wannan tattaunawa da aka yi da tsigaggen Sakataren APC na Kasa, kwana biyu kafin sauke shi da sauran shugabannin jam’iyyar, Waziri Bulama ya bayyana irin kokarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi domin magance rikicin jam’iyyar APC a Jihar Edo, kuma ya yi wasu bayanai masu muhimmanci, kamar yadda yadda za a karanta a ji.
PT: Ko ka na ganin jam’iyyar APC za ta iya fita har ta tsira daga wannan kacamewar rikici kuwa?
BULAMA: Wannan rigingimu da ake ji kuma ake gani a cikin APC, ba za su zama wata barazana ga jam’iyyar ba. Har yanzu kan ‘ya’yan jam’iyyar a hade ya ke. APC a yanzu haka ta na da mambobi masu rajista har milyan 16 a kasar nan.
Tun daga karabitin mamba har zuwa masu rike da mukamai, har ta kai ga Shugaba Muhammadu Buhari, to milyan 16 din nan duk kan mu a hade ya ke.
Don haka ina tabbatar maka babu wata barazana ko baraka ko bangarancin wasu da suka balle.
Ita jam’iyya wani gungu ne na gamayyar mutanen da suka taru a karkashin inuwa daya, masu muradi daya.
Babban muradin shi ne a samu nasarar takarar shiga zabe kuma a yi nasara. Duk wasu dalilai kuwa sun biyo bayan wannan muradin ne.
PT: Kai ka na cewa kan ku a hade ya ke. Amma kuma ga rigingimu na ta kara dabaibaye ku, har wasu na rikici kan halascin rikon Shugabancin jam’iyya.
BULAMA: Zan iya cewa tun farko tsarin tafiyar shugabannin jam’iyyar ne ya shafe shekaru ba ya wata kazarniyar motsa jam’iyya har ya rika magance duk wani kalubale da ya taso na bukatun mambobin jam’iyya.
Saboda idan ka duba, shi kan sa ofishin Babban Sakatare na Kasa ya kasance holoko kusan shekara daya da rabi. Shi ne dama ke gudanar da ayyukan da za su motsa dukkan bangarori na ayyukan jam’iyya.
To saboda kowane bangaren kwamitoci na jam’iyya zaune ya ke turus, ba aikin komai da ke gudana, sai aka fara kananan maganganu, har abin ya kai ga fusata da damuwa sosai. Dalili kenan wasu suka fara kiraye-kirayen a yi taron NEC na Kasa. NEC shi ne Kwamitin Tsare-tsaren Zartaswa. Gudanarwa kuwa duk aikin Kwamitin NWC ne.
Wadani kwamitoci biyu kadai ake ta magana a kan su. An manta akwai kwamitoci har 14 daga Mazaba zuwa Shiyya da ba su aikin komai tsawon lokaci.
PT: Ana cewa dama Buhari ne igiyar da ta daure tsintsiyar APC. Kuma da ya sauka daga mulki, tsintsiyar tarwatsewa za ta yi. Me za ka ce game da wannan maganar?
BULAMA:Tabbas kowa ya San Buhari ne igiyar da ta daure tsintsiyar. Amma ba za a ce za ta tarwatse ba idan ya kammala wa’adin mulkin sa. APC ta tattaro mutane masu akidu irin na sa.
Ko ya tafi jam’iyya ta na nan. Ai har ma ya sa kafa daya a waje, domin ya ce ba zai sake tsayawa takara ko ya tsaya wa wani lallai sai ya tsayar da shi ba.
To ai wannan ne ma babban dalilin da ka ga wasu abubuwa na bijirowa a cikin APC. Wasu ne masu ganin cewa su na da wata manufa ta batun takarkarun zabuka ke neman karbe ragamar jam’iyyar, domin su ji dadin karkata akalar ta yadda muradin su ke so, bayan Buhari. Amma dai na san APC za ta tsallake wannan siradin.
PT: Yanzu me ka ke gani ita ce hanya mafita. Ganin cewa ku na fama da tulin kararraki a kotu?
BULAMA: Wato akwai mutane masu manufofi daban-daban a cikin APC. Wasu mulki su ke so wurjanjan. Wasu kuma al’umma su ke so su ga an inganta. Wasu aiki su ke nema. Kowa da na sa bukatun daban-daban.
Na fada maka a baya jam’iyyar zaman dirshan ake yi ba a komai. Amma daga lokacin da na karbi aikin Sakatare kwanan baya, na motsa jam’iyya. Aiki na ke ta yi kusan awa 15 kullum babu hutu.
Batun shari’u a kofu kuwa akasarin su duk na son kai da son rai ne ke sa wasu na kai karar ko a kai su.
Ya kamata a ce jam’iyya na aiki kamar wata cikakkar ma’aikata ko hukuma mai cikakkun manufofi da alkibla. Yadda ko shugaba ko na kusa da shi ba ya nan, ayyuka ba za su tsaya ba.
Ka ga kamar idan shugaban kasa ba ya nan, ayyuka ba tsayawa suke yi cak ba. To abin da na ke nufi kenan.
PT: Yanzu bari mu tabo batun rikicin siyasar Jihar Edo. Ka na ganin APC za ta yi nasara kuwa a Edo? Ba ka ganin abin da ya faru Edo zai faru a wasu jihohi?
PT: Ni ban ga wata gagarimar matsala a APC ba. Sai dai surutai na mutane kawai daga Edo da surutai da Ondo.
Ko da rikici tsakanin Obaseki da Osbiomhole ko babu, ko Osbiomhole ke shugabancin ki ba shi ba, akwai wasu kananan rikice-rikicen da suka raba kawunan wasu a jam’iyyar. Mun gode Allah, tunda Obaseki ya fice daga APC din.
Wannan sabani da ka ke gani, matsala ce ta cikin gida kawai. Kuma ka san komai nufin Allah ne. Duk abin da Allah ya kaddara zai faru, to sai fa ya faru din.