Kakakin Yada Labarai na tsohon Gwamnan Jihar Oyo, Abiola Ajimobi, mai suna Bolaji Tunji, ya yi karin haske dangane da yadda marigayin ya yi musu bankwana da nufin zuwa Abuja domin halartar wani taron da ya danganci halin da siyasar jam’iyyar APC ke ciki.
A tafiyar ce ya kamu da ciwon da ke da nasaba da cutar Coronavirus, wadda ta kwantar da shi tsawon wata daya. A karshe ya rasu a wani asibiti a Lagos, ranar Alhamis da ta wuce.
Bolaji ya yi rubutun sa a matsayin bankwana da Marigayi Ajimobi, a shafin sa na Facebook, a yau Juma’a.
AJIMOBI: Tafiyar da babu dawowa har abada:
1. Mu na tare da shi aka yi masa kiran gaggawa zuwa wani muhimmin taron da ya shafi jam’iyya.
2. Saboda kira ne a uzurce, babu halin ya tafi tare da mu gaba-daya, domin shatar karamin jirgin sama zai yi.
3. Bai kwashi zugar ‘yan rakiya ba, sai jami’an tsaron sa kadai ya tafi tare da su.
4. Ya bar duniya ya na cikin shirin komawa Abuja da zama. Kamar yadda yadda ya shaida mana cewa a can zai tare, tunda dai an dora masa mukami a jam’iyya, shi ne Mataimakin Shugaba na Shiyyar Kudu, kuma Shugaban Kwamitin Sasanta Rikice-rikice.
5. Babu wani ko wata alamar cuta ko ciwo a jikin sa. Lafiyar sa kalau, ba ya koken wata lalura na damun sa.
6. Ga shi dai dan shekara 70 a duniya, amma garau ya ke, jikin sa bai nuna ya yi tsufan dattijo mai shekaru 70 ba.
7. Har yanzu mu na al’ajabin sanadiyyar mutuwar sa, saboda mutum ne mai kaffa-kaffa da taka-tsantsan da lafiyar sa.
8. Idan ya na gida ko ofis, ko zai shiga wani wuri, ko da yaushe ya na sa takunkumi a bakin sa. Kuma ba ya shiga cikin rintsin jama’a. Sannan ba ya yarda a matse shi kusa-da-kusa.
9. Saboda mun san shekarun sa sun kai sosai, ba mu wasa da mika masa ruwan sabulun wanke hannu, a duk lokacin da ya taba wani abu.
10. A ofis muna da wurin wanke hannaye har uku kafin a kai ga shiga farfajiyar ofishin. Sai mutum ya wanke a ‘gate’, a ciki sai an wanke. Haka idan za a shiga ofis akwai wurin wanke hannaye.
11. Shin wai ya aka yi aka samu akasi ne? A ina aka samu kuskure? A ina wannan mummunan al’amari ya same shi?
12. Tun bayan da ya kammala zangon sa na biyu, ya so ya zauna ya huta, amma saboda ya na son ya amfana wa jama’ar sa, sai ya karbi tayin zama cikin shugabannin jam’iyya da aka yi masa.
13. Yayin da ya kwanta ciwo a asibiti, ban taba tunanin ciwon ajali ba ne. Na yi yakinin cewa zai warware ya warke, kuma ya tashi.
14. Akwai abubuwa masu muhimmanci da tarin yawa, wadanda ya shirya zai cimma a rayuwar sa. Kuma duk na amfanuwar jama’a ne.
15. Ban san cewa ba zai cimma wadannan kyawawan kudirori da ya sa a gaba ba.
16. Duk da gangunan da ake yi maka kida sun fashe a ranar Alhamis, har yanzu karar sautin amon kidan na tashi. Ba kuma za mu daina jin dadin sautin wannan kidan ba, har mu ma Mai kasancewa ta kasance a kan mu.
17. Maigida na Ajimobi ina Yi maka bankwana. Allah ya gafarta maka. Ya sa mutuwa hutu ce.