Jaririya’yar wata biyu ta kamu da Korona

0

Idan ba a manta ba, makonni biyu kenan da gwanatin Kaduna ta sanar da warkewar wata jaririya ‘yar wata hudu a jihar.

A jihar Delta, an samu wata ‘yar wata biyu, da gwaji ya nuna ta kamu da cutar.

Kwamishinan kiwon lafiyar jihar, Mordi Ononye, ya bayyana cewa wannan jaririya na daga cikin wadanda suka kamu da cutar 116 a jihar.

Ya kara da cewa ma’aikatan asibiti na duba wannan jaririya domin sama mata lafiya.

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 350 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Alhamis.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Alhamis, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 102, Ogun – 34, FCT – 29, Borno – 26, Kaduna – 23, Rivers – 21, Kwara – 16, Ebonyi – 17, Katsina – 14, Edo – 10, Delta – 10, Kano – 10, Bauchi – 10, Bayelsa – 9, Imo – 8, Plateau – 4, Ondo – 3, Nasarawa – 2, Gombe – 1, and Oyo – 1

Yanzu mutum 11,516 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 3535 sun warke, 323 sun mutu.

Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.

Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.

A ranar Alhamis kawai, jihar Legas ta samu karin mutum sama da 100.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 5, 542, Kano – 980, FCT – 792, Katsina – 385, Edo – 351, Oyo – 318, Kaduna – 320, Borno – 322, Ogun – 316, Jigawa – 274, Rivers – 290, Bauchi – 256, Gombe – 170, Sokoto – 115, Kwara – 127, Plateau – 113, Delta – 116, Nasarawa – 90, Zamfara – 76, Ebonyi – 80, Yobe – 52, Osun 47, Akwa Ibom – 45, Adamawa – 42, Niger – 41, Imo – 47, Kebbi – 33, Ondo – 36, Ekiti – 25, Enugu – 24, Bayelsa – 30 Taraba – 18, Abia–15, Benue – 13, Anambra – 12, and Kogi – 3

Share.

game da Author