Jami’an kiwon lafiya 812 suka kamu da Coronavirus

0

Shugaban Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) Chike Ihekweazu ya bayyana cewa ya zuwa yau jami’an kiwon lafiya da likitoci har 812 ne suka kamu da cutar Coronavirus a kasar nan.

Da ya ke bayani a wurin taron manema labarai a ranar Talata, ya ce 29 daga cikin likitocin duk Ma’aikatar NCDC ne.

“Takwas daga cikin su kuwa duk a yanzu haka su na Cibiyar Killace Masu Cutar Coronavirus a Idu, Abuja.”

Ihekweazu ya kara da cewa NCDC na ci gaba da raba wa jami’an kula da lafiya da likitoci kayan kariyar jiki daga kamuwa da cutar Coronavirus.

“Mun raba kimanin kayan kariya har 40,000, kuma za mu ci gaba da rabawa babu kakkautawa.”

“Zuwa karshen wannan makon, kayayyakin za su kara isa a dukkan Manyan Asibitocin Gwamnatin Tarayya da ke fadin kasar nan.”

Ya zuwa ranar 30 Ga Afrilu, guda 113 kadai suka kamu. Wannan na nufin kusan 700 sun kamu a cikin wata daya kenan.

Ya ce sai jami’an kula da lafiya masu horo kan cututtuka masu yaduwa ne kadai aka amince su kula da masu cutar Coronavirus.

Amma an umarci asibitoci masu zaman kan su da ke son kula da masu cutar Coronavirus su yi rajista da NCDC, wato dai da Ma’aikatar Lafiya ta jihar da asibitin ya ke.

Rahotanni da dama sun nuna likitoci da jami’an lafiya da dama a kasar nan su na cikin hadarin kamuwa da cutar Coronavirus.

Wasu ma har ta kai su ga rasa rayukan su, kamar yadda rahotanni daga jihohi suka tabbatar.

Wata matsala kuma ita ce karancin kudaden alawus da har sai da ta kai ga wasu jihohin likitoci da jami’an kula da lafiya na barazanar yajin aiki.

Share.

game da Author