Iran ta raba sammacin a kamo mata Shugaban Amurka Donald Trump

0

Iran ta fitar da sammacin neman a kamo mata Shugaban Amurka Donald Trump, bisa dalilin kisan Babban Kwamandan Iran, Qassem Soleimani.

Trump ya bayar da umarnin kisan Soleimani a cikin kasar Iraq a wata ziyara da ya kai kasar daga Iran.

An kashe shi a lokacin da ya ke cikin jirgin sama tare da wasu shugabannin Iraki a cikin jirgin.

Trump ya zargi Soleimani da laifin hada hare-hare a kan Amurkawa a wasu kasashe.

A ranar Litinin ne mahukuntan Iran suka sanar da cewa sun roki ‘yan sandan kasa-kasa cewa su bada hadin kai da Trump ya keta kasar su, to su damke shi su auna zuwa Iran.

Kasar Iran na tuhumar Trump da laifin kisan kai da ta’addanci.

“Amma da wahalar gaske a biya wa Iran wannan bukata, domin ‘yan sandan ‘Interpol’ ba su shiga sha’anin rikice-rikicen siyasa.” Haka gidan talbijin na Aljazeera ta bayyana.

Wata kotun Iran ta yanke hukuncin kisa a kan wani dan kasar mai suna Mahmoud Mousari Majid.

An zarge shi tare da kama shi da laifin tona asirin da gulmata wa sojojin Amurka da Israila inda Qassem Soleimani ya ke, har aka samu nasarar kai masa hari da ‘drone’, aka tarwatsa jirgin da ya ke a ciki.

Share.

game da Author