IFAD za ta raba wa manoma da al’ummar karkara dala milyan 40 domin noma abinci

0

Kwanaki kadan da Hukumar IFAD ta bayyana fargabar cewa mutanen da yunwa za ta kashe a Afrika za su haura wadanda Coronavirus za ta kashe, yanzu kuma IFAD ta ce ta ware dala milyan 40 domin tallafa wa manoma da mutanen karkara karfafa noma yadda za a kauce wa barkewar yunwa.

Shugaban Hukumar Cibiyar Bunkasa Manoman Karkara ta Majalisar Dinkin Duniya (IFAD), Gilbert Hungbo ne ya bayyana haka a cikin wani rahoto da hukumar ta fitar kwanan nan.

Ya ce baya ga wadannan dala milyan 40 wadanda tuni an tanade su, IFAD ta kuma kafa gidauniyar karbar gudummawa ta jimlar dala milyan 200 daga mambobin kasashen IFAD, cibiyoyin bayar da tallafi na duniya da kuma hamshakan ‘yan kasuwa da kamfanoni.

“Lokaci ya yi da za mu zabura mu yi wani kokarin kauda matsalolin da annobar Coronavirus na haddasa mummunar annobar yunwa da karancin abinci.

“Irin yadda Covid-19 ta ragargaza tattalin arziki a duniya, sannan ta hana manoma katabus ta hanyar kasa noma da hana zirga-zirgar sayar da amfanin gona, tabbas hakan zai haddasa bala’in karancin abinci da yunwa a duniya.

“Yunwa kuwa ta na afka wa al’umma musamman a karkara da wasu masifu da suka haka da tilasta su yin hijira zuwa inda bai kamata su yi rayuwa ba.

“IFAD za ta taimaka wa manoma da al’ummar karkara bunkasa noma, kiwo da kuma kamun kifi. Za a samar musu hanyoyin sayar da amfanin gonar su a lokacin kasa fita zirga-zirga a kasuwanni, saboda Coronavirus. Kuma za a samar musu da hanyoyin samu iri, takin zamani da sauran matakan bunkasa noma yadda za a samu albarkar noma sosai.” Inji Houngbo.

IFAD ta ce cutar Coronavirus ta rafki manoma sosai, kuma akwai alamun annobar farin-dango. Sannan kuma an duskanci canji da gurbacewar yanayi, ga kuma uwa-uba rikice-rikice da kashe-kashe a wasu kasashe, inda sanadiyyar hakan, manoman karkara ba su ma iya fita gonaki domin ci gaba da noman su.

Fargabar Barkewar Yunwa Sanadiyyar Coronavirus:

Cibiyar Bunkasa Harkokin Noma ta Duniya (IFAD), ta bayyana cewa akwai wasu karin akalla mutane milyan 23 da yunwa za ta kassara a Kasashen Yankin Saharar Afrika, a cikin shekarar 2020.

Shugaban IFAD Gilbert Houngbo ne ya bayyana haka a wurin taron Zauren Tattauna Tattalin Arziki, na World Economic Forum.

Taron na bana an tattauna matsalar Hanyoyin Tattalin Abinci A Afrika, a lokacin annobar Coronavirus.

Houngbo ya ce nazari, hasashe da kirdadon yadda ake fuskantar matsalar abinci, ya nuna cewa a shekarar 2020 wadanda yunwa za ta kashe a yankin Afrika za su zarce wadanda cutar Coronavirus ta kashe, nesa ba kusa ba.

IFAD dai cibiya ce wadda ta shahara wajen tallafa wa mutanen da ke zaune a karkara wajen bunkasa noma, kara samar wa ‘ya’yan su abinci mai gina jiki da kuma samar wa kan su kudaden shiga ta hanyar noma.

Houngbo ya ce Coronavirus ta nuna cewa akwai hagarimar matsalar tsarin samar da abinci, raba shi da kuma gyarawa.

Manoma da dama na kokawa da yadda ba su iya samun taking zamani saboda dokar hana zirga-zirga.

Sannan kuma ba su iya zuwa gona kuma wadanda suka noma amfanin gona na sayarwa, an rufe kasuwanni ballantana su rika sayar da amfanin gonar su.

Rahoton ya kara da cewa a shekarar 2019 yunwa ta kassara mutum milyan 135 a duniya, wadanda milyan 73 daga cikin su sun fito daga Afrika, cikin kasashe 36.

A Arewacin Najeriya yunwa ta kassara mutum milyan 5 a 2019.

Idan ba a manta ba, PREMIUM Times ta buga rahoton yadda farin-dango suka darkako Afrika ta Yamma daga Gabas.

Share.

game da Author