ICPC ta kwace katafaren kadara mallakin gwamnan Bauchi, Bala da yayi karfakarfar mallaka a Abuja

0

Hukumar ICPC ta kwace wani katafaren kadara mallakin gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da ya karbe da ake zargin ya karbe da karfin mulki a lokacin na ministan Abuja ya baiwa wata makaranta mai suna Zinaria.

Bincike dai ya nuna cewa shi da wasu yan uwansa ne ke da mallakin wannan makaranta.

ICPC ta ce wannan fili mallakin ma’ikatan ayyuka gona ne amma yayi karfa-karfa ya kwace filin.

Wannan kadara na, Plot 298 Wuye a Abuja.

Hukumar ta kara da cewa nan ba da dadewa ba za ta aika wa wadanda ke iko da filin yace takardar mika filin ga gwamnati.

Gwamna Bala Mohammed

Idan ba a manta ba nasarar da sanata Bala Mohammed yayi a zaben 2019 ya kubutar da shi daga fuskantar tuhume tuhumen hukumar EFCC da ICPC a kotu a dalilin zargin harkallar da ya tafka a lokacin yana ministan Abuja.

Tun bayan saukarsa daga kujerar ministan Abuja, ya rika fuskantar sammaci daga kotu bisa kararrakin da EFCC ta shigar na yin babakere, da sama da fadi da kadarorin gwamnati.

Kwasam kuma sai yayi nasara a zaben 2019 inda ya doke gwamna mai ci na jam’iyyar APC, a zaben.

Yanzu dai sai dai a ambata babi tuhuma domin dikar kasa ta bashi kariya a matsayin sa na gwamnan.

Koma menene dai sai ya sauka daga wannan kujera za a karkare.

Share.

game da Author