HASKEN LANTARKI: Buhari ya yi alkawarin samar da 11,000kv nan da 2023

0

A cikin alwashin da Shugaba Muhamamdu Buhari ya kara sha wa ‘yan Najeriya, ya bayyana cewa nan da shekarar 2023, gwamnatin sa za ta wadatar wa kasar nan da makamashi mai karfin hasken lantarki har 11,000.

Buhari ya yi wannan kudirin ne a ranar Juma’a cikin jawabin sa na Ranar Dimokradiyya, wadda ta kasance ta farko da aka taba yin bikin ta a ranar 12 Ga Mayu, maimakon 27 Ga Mayu da aka saba.

Buhari ya bayyana wasu muhimman ayyukan inganta karfin wutar lantarki da ya ce Gwamnatin sa na kan gudanarwa.

Ya ce ana kan aikin bunkasa lantarki na Alaoji zuwa Anacha, sai na Cibiyar Samar da Lantarki/Makamashi ta Delta zuwa Benin da Kaduna da kuma Kano.

Akwai kuma aikin lantarki a Lagos zuwa Ogun, sai kuma na Abuja Babban Birnin Tarayya da kuma aikin bunkasa wuta na shacin Arewacin kassr nan.

Da ya ke magana dangane da yadda karfin lantarkin zai kai har Miga wat 11,000 kv, Buhari ya ce za a cimma wannan adadin ne ta hanyar yarjejeniyar aikin makamashi da aka kulla tsakanin Najeriya da kamfanin kasar Jamus, wato Siemens.

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Buhari ta fara kamfe da aikin tashar harken lantarki ta Mambilla tun a cikin 2017.

Ga yadda ake kururuta aikin, milyoyin ‘yan Najeriya da dama sun dauka ma an kusa kammala aiki, saura kyalla wuta kawai a ga harke ko’ina a Arewacin kasar nan.

Sai dai kuma bayan raba Ma’aikatar Harkokin Makamashi daga hannun tsohon Ministan Ma’aikatar, Raji Fashola, sabon Ministan Makamashi Sale Mamman ya fito baro-,baro ya ce ko ma filin ba a share ba.

A bisa dukkan alamun yadda aikin ke tafiya, ganin ko farawa ba a yi ba har yanzu, da wahalar gaske a ce an kammala aikin nan da shekara uku.

Musamman ganin yadda cutar Coronavirus ta kara taka wa ayyuka dama burki a Najeriya da duniya baki daya.

Share.

game da Author