Mazauna kauyen Ruwan Tofa dake jihar Zamfara sun shaida cewa duk da sun sanar da jami’an tsaro cewa mahara za su diran wa kauyen, maharan ba su fasa ba, sun zo din kuma sun kashe mutane son ran su babu keyar ko jami’i daya da ya kawo wa mutane dauki.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda mahara suka afka wa kauyen Ruwan Tofa dake jihar Zamfara, inda suka kashe akalla mutum 10.
Sai dai kuma mazauna kauyen da suka zanta da wakilin mu sun shaida cewa mutum 23 maharan suka kashe.
Daya daga cikin hadiman gwamnan jihar, Mu’azu Yusuf ya bayyana cewa wannan hari shine mafi muni cikin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai wannan kauye tun shekaru uku da ayyukan ta’addanci yayi muni a jihar Zamfara.
Yusuf yace da kansa ya kira kwamishin tsaro na jihar Abubakar Dauran, ya shaida masa sakon maharan, sannan kuma ya kira shugaban rundunar sojoji da ke aiki a wannan yanki, hakazalika ya garzaya fadar sarkin garin Dansadau domin sanar masa sakon ‘yan ta’addan domin jami’an tsaro su kawo tsaro.
Amma sai bayan maharan sun yi barnar da za su yi ne jami’an tsaro suka bayyana.
Dauran ya ce tuni an aika da jami’an tsaro su kai wa mutanen kauyen dauki. Sannan ya ce mutum 14 suka rasu ba 23 ba, amma kuma bai karyata korafin Yusuf ba cewa an sanar da su kafin diran ‘yan bindiga.
Discussion about this post