Hadarin Girman Kai, Jiji Da Kai Da Raina Mutane, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mabuwayi, tsarkkaken Sarki. Tsira da aminci su tabbata ga fiyyayyen halitta, Annabin karshe, Annabi Muhammad (SAW), da alayensa da Sahabban da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa har zuwa ranar sakamako.

Ya ku bayin Allah, wallahi, har kullun, ni dai ni kan yi mamaki idan na kalli dabi’u da halaye na wasu mutane, wadanda Allah ya jaraba da mummunar dabi’ar nan ta girman kai da jiji da kai da wulakanta mutane, ko kuma daukar mutane ba bakin komai ba.

Ya ku jama’ah, wallahi wadannan dabi’u munana ne ga ko wane Musulmi, ko ma in ce ga ko wane dan Adam, amma dai sun fi muni ga malamin addinin Musulunci, ko kuma wanda ya kira kan sa malami. Sam bai kamata ace malami ya tasirantu da wadannan dabi’u ba! Domin duk malantar malami da zarar Allah ya jarabe shi da wadannan dabi’u, to sai ka ga ya zama shirme wallahi.

Haba jama’ah, ace wai saboda girman kai da jiji da kai da raina mutane, sai ka ga mutum wai shi ba zai bari ace shi malami ba ne, a’a, da karfi da yaji sai ya nuna shi malami ne, wasu kuma ba malamai bane, wace irin dabi’a ce wannan? Kuma duk wannan ba komai yake jawo shi ba Illa, بطر الحق da غمط الناس wato KIN GASKIYA DA WULAKANTA MUTANE KO RAINA SU. Ina rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala ya shirye mu, amin.

Ya ku bayin Allah, wallahi girman kai da jiji da kai, da wulakanta mutane dukkansu dabi’u ne munana wadanda addinin Musulunci ya yake su, kuma dabi’u ne ababen zargi masu kai mutum ga halaka cikin kankanin lokaci, banbanci da ke tsakaninsu kadan ne kamar haka:

Daga cikin alamun girman kai dai sun hada da, ka rinka ganin fifikon kan ka akan wani, ka rinka jin kafi wane, kai abu kaza ne, kafi karfin ko kuma ka wuce matsayin wane, kafi karfin sauraronsa, kafi karfin a hada ka da shi, da dai makamantan haka. Jama’ah kun ga a irin wadannan dabi’u babu tawadu’u, babu koyi da rayuwar Annabi (SAW) a cikin malanta, alhalin duk wani malami, komai girman sa, Annabi (SAW) yake gado kuma shine abun koyin sa; bai isa ya wuce gaban Annabi (SAW) wurin malanta ba, da zarar kuma yayi hakan, to sai muce ya halaka, Allah ya shirye shi!

Hoton rayuwar Manzon Allah (SAW) ita ce abun koyin mu, Annabi (SAW) shine abun son mu kuma abun kaunar mu.

Shi ma misalin jiji da kai shine, ka rinka jin kana da wani abu da waninka ba ya da shi. Dukkansu dai munanan laifuka ne da suke dauke bawa daga godewa Allah zuwa godewa kai, da jin cewa wayon mutum ko iyawarsa sune suke yi masa abu. Sannan suna hana mutum yabon Allah da gode masa kamar yadda ya kamata, sai mutum ya koma yabon kan sa, da mamakin kan sa, da kuma kin kaskantar da kai ga Mahalicci, da ruduwa da kai, da kin girmama mutane, da sanin matsayinsu, zuwa hantararsu, da danne masu hakkokinsu.

Sannan na daga illolin da jiji da kai yake haifarwa, akwai rusa ayyuka kyawawa, da kuma boye masu kyau, da kuma jawo zarge-zarge, da rashin yarda da rashin aminci tsakanin mutane.

Sannan hukuncin jiji da kai dai mun san haramun ne a Musulunci, domin nau’i ne na shirka kamar yadda malamai suka bayyana. Shaikhul Islam Ibn Taimiyyah yace:

“So da yawa riya tana da kusanci da jiji da kai. Ita riya tana babin shirka da halittu, shi kuma jiji da kai yana babin shirka da kai, wannan shine halin mai girman kai, mai riya, wanda bai tabbatar da fadin Allah madaukakin Sarki ba:
“ﺇﻳﺎﻙ ﻧﻌﺒﺪ”

Mai jiji da kai kuma bai tabbatar da fadin Allah madaukin Sarki ba, wato:
“ﻭﺇﻳﺎﻙ ﻧﺴﺘﻌﻴن”

Duk wanda ya tabbatar da fadin Allah “ﺇﻳﺎﻙ ﻧﻌﺒﺪ” zai fita daga riya, wanda kuwa ya tabbatar da fadin Allah
“ﻭﺇﻳﺎﻙ ﻧﺴﺘﻌﻴﻦ”
Zai fita daga jiji da kai.”

Ya ku jama’ah, lallai dabi’ar jiji da kai abun zargi ne a cikin Alkur’ani da Sunnah. Allah Madaukakin Sarki yace:

“ﻭﻳﻮﻡ ﺣﻨﻴﻦ ﺇﺫ ﺃﻋﺠﺒﺘﻢ ﻛﺜﺮﺗﻜﻢ ﻓﻠﻢ ﺗﻐﻦ ﻋﻨﻜﻢ ﺷﻴﺌﺎ”

Ma’ana:

“Da ranar yakin hunaini, lokacin da yawanku ya burge ku, kuma bai tsinana maku komai ba.

Abdullahi Dan Mas’ud yace:

“Halaka tana cikin abubuwa biyu: cire tsammani daga Allah da kuma jiji da kai.”

Ya ku bayin Allah, ku sani, wallahi hadarin jiji da kai ya kai hadari, domin idan ba ayi hankali ba yakan kai mai yin sa zuwa ga kafirci da fita daga addinin Musulunci, kamar yadda shaidan yayi alfahari da asalinsa, da ibadarsa, wannan yasa yayi wa Allah girman kai, kuma ya halaka.

Imam Ibn Qudamah yace:

“Ka sani jiji da kai yakan kawo girman kai, domin yana cikin dalilan da ke kawo girman kai, a cikin girman kai kuwa akwai masifu da yawa, akwai tsakaninka da halittu da kuma tsakaninka da mahaliccinka.”

• Abubuwan da suke sa a gane mai jiji da kai, kuma da zarar mutum yana da su, to lallai Allah ya jarabe shi da wadannan munanan dabi’u, sune kamar haka:

1. Kin gaskiya, da kin karbar ta, da kuma hantarar mutane.

2. Raina mutane.

3. Rashin shawartar masu hankali da manya a cikin al’amurra.

4. Yin rangwada, takama ko yanga a cikin tafiya, da nuna ji da isa.

5. Ganin girman biyayyar da mutum yake yiwa Allah, da kuma ganin yawanta.

6. Alfahari da ilimi da kuma yin gori dashi.

7. Alfahari da dukiya da dangi da kyawun halittar mutum.

8. Raina kokarin wasu Malamai masu ikhlasi da tsoron Allah.

9. Dawwama akan kuskure da kin karbar gyara.

10. Karancin sauraron ilmi ko mika wuya ga masu shi, da lazimtarsu, ko kuma kokarin yaudarar kai cewa shi yanzu ya gama karatu, alhali wannan karya ce.

11. Aga cewa kullun mutum yana hantarar masu sabo da masu zunubi, maimakon kokarin shiryar da su su daina.

12. Manta zunubai, da raina su, da ganin karancinsu.

13. Kokarin sabawa sauran mutane da gangan, don jin isa ko nuna isa.

• Abubuwan da ke janyo jiji da kai:

1. Jahilci.

2. Karancin tsantseni da tsoron Allah.

3. Raunin jin cewa Allah yana tare da kai kuma yana kallon ka.

4. Karancin wadanda za suyi wa mutum nasiha.

5. Mummunar niyyah.

6. Mutum ya rinka yawan jin dadin yabon mutane, ko kuma yin abu don samun yabon su, da kuma taimakon shaidan akan haka.

7. Fitinuwa da son duniya, da bin son zuciya.

8. Karancin tunani.

9. Karancin godewa Allah.

10. Karancin Ambaton Allah.

11. Rashin tadabburin Alkur’ani da kuma Hadisai.

12. Amintuwa da azabar Allah da dogara da afuwarsa da gafarar sa kadai.

Daga karshe, ‘yan uwa Musulmi, maganin girman kai da jiji da kai, da wulakanta mutane, ko raina su, shine, tuna ni’imomin Allah a kan mu, da kuma tuna yadda mutum yake a baya kafin ya kai matsayin da yake a halin yanzu, da kuma tuna tarihin al’ummomin da suka gabata, da kokarin karanta rayuwar Manzon Allah (SAW) da Sahabbansa, tare da kokarin yin koyi da su.

Ya Allah, muna tawassali da sunayenka tsarkaka, ka tausaya muna, ka karbi tuban mu, ka azurta mu da hakuri, juriya, jajircewa da ikon cin jarabawarka a duk inda muka samu kawunan mu, amin.

Ya Allah, kayi muna gafara, ka shafe dukkan zunuban mu, don son mu da kaunar mu ga fiyayyen halitta, Annabin rahmah (SAW).

Ina rokon Allah ya kyauta, ya kawo muna mafita ta alkhairi, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Share.

game da Author