Ministan Sufurin Jiragen Sama Hadi Sirika, ya bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta amince a biya naira bilyan 1.7 ladar zanen taswirar sabon titin sauka da tashin jiragen sama a Babban Filin Nnamdi Azikwe International Airport.
Duk da cewa shi ne filin jirgin saman da Najeriya ke tutiya da shi baya ga na Murtala Mohammed da ke Lagos, filin na Abuja har yau titin saukar jirage daya kwal ya ke da shi.
Sirika ya yi wannan bayani ne a Fadar Shugaban Kasa bayan kammala taron Majalisar Zartaswa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba.
Minista Sirika dai bai yi wa ‘yan jarida bayanin tsawon titin ba, kuma bai bayyana sunayen kamfanonin da za a bai wa aikin zanen taswirar titin kwaya daya tal ba.
Sai dai ya an bada kwangilar zanen a farashin dala daidai da naira 360. Sannan kuma akwai kudaden harajin-jiki-magayi (VAT) har kashi 7.5% a ciki.
Kusan watanni uku kenan filayen jiragen sama na rufe. Amma gwamnatin tarayya ta sanar da ware wasu filaye biyar da ya ce za a fara budewa a ranar 20 Ga Yuni.
Discussion about this post