Gwamnatin Kaduna ta rufe makaranta mai zaman kanta da ta yi wa dokar Korona ‘Kunnen Uwar Shegu’

0

Ma’aikatar Ilimi na jihar Kaduna ta rufe fitacciyar makaranta mai zaman kanta a Kaduna da ta karya dokar Korona ta gayyaci dalibai yin jarabawar shiga makarantar.

Darektan hukumar kula da makarantu masu zaman kansu ta jihar, Umma Ahmed, ta shaida wa Kamfanin dillancin Labarai cewa za a kuma karbe lasisin wannan makaranta.

Umma ta bayyana cewa da gangar wannan makaranta ta karya dokar gwamnati, inda ta gayyaci dalibai su zo su rubuta jarabawa.

” Ko da muka isa makarantar mun iske dalibai kusan 70 suna rubuta jarabawa da malamai 35 suna kai komo. Sannan kuma da ma’aikata suna aikin gini a makarantar suna aikin su. Za a janye lasisin wannan makaranta.

” Daliban ba su saka takunkumin fuska ba. Duk mun umarci iyaye su garzayo makarantar su tafi da ‘ya’yan su.

Umma ta kara da cewa gwamnatin tarayya bata janye dokar bude makarantu ba sannan ko a jihar ma ba a janye dokar ba.

” A kullum muna tattaunawa da kungiyar masu makarantun masu zaman kansu na jihar domin tsara yadda za a dawo makarantu. Tare ake komai da su sun sani amma ita makarantar Future Leaders tayi wa gwamnatin Najeriya kunnen Uwar Shegu ta gayyaci dalibai suka zo har jarabawa suke yi, sannan babu wani kariya da aka tsara musu.

Shugaban kungiyar masu makarantun masu zaman kansu na jihar Kaduna, Philip Iorhena, ya bayyana cewa lallai gwamnati na aiki tare da kungiyar tun lokacin da aka garkame jihar. Wannan abu bai yi mana dadi ba.

” Za mu ci gaba da tausa gwamnati ta yafe wa wannan makaranta da ta karya doka.

Share.

game da Author