Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Kwamitin Binciken rikicin adddinin 1992 da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 2,000 a garin Zangon Kataf.
Wata sanarwa da Kakakin Yada Labaran Gwamna Nasir El-Rufai, Muyiwa Adekeye ne ta bayyana haka.
“Rikicin addinin da aka yi cikin watan Fabrairu, 1992 a Zangon Kataf, ya yi sanadiyyar asarar rayuka 95 da raunata mutum 223. An kara yi a cikin watan Mayu, 1992, wanda wadanda suka rasa rayukan su suka kai 1,528 a Karamar Hukumar Zangon Kataf da wasu mutum 305 a Zaria, Ikara da wasu sassan Jihar Kaduna.”
Haka sanarwar da Adekeye ya fitar kuma ya turo wa PREMIUM TMES ta nuna.
Duk da an kafa kwamitin bincike a baya, gwamnatocin da suka gabata ba su yi aiki da rahoton bayanan kwamitin binciken ba.
To sai kuma wani riki makamancin wannan ya faru a yankin a cikin wannan wata na Yuni.
“Abin takaici ne matuka cewa daya daga cikin dalilan da suka haddasa wancan rikici na 1992, shi ne dai kuma musabbabbin na wannan wata, shekaru 28 bayan wancan na farko.
Rikicin Baya-bayan Nan
Mummunan rikici ya sake barkewa a ranar 11 Ga Yuni, 2020 a kan rikicin gonar da aka taba yin rikici sanadiyyar ta tun cikin 1992. Kuma kwamitin Bincike na 1995 ya yi magana a kan gonar.
Sakamakon binciken da kwamitin da aka nada a wancan lokacin a karkashin mulkin gwamnan jihar a wancan lokaci, Dabo Lere ba a yi komai a kai ba, hakan ya sa gwamnatin da ta gaje ta ta Kanar Ja’afar Isah, ta kafa wata kwamitin domin sake duba musabbabin rikicin 1992.
Bayan rikici ya barke a 1992, Gwamnatin Ibrahim Babangida ta kama wasu ta tsare, ciki kuwa har da wadanda aka gurfanar kotu aka yanke wa hukunci. Sai dai gwamnatin Dabo Lere bata iya fidda takarda da zai nuna wa duniya cewa ita ga matsayarta ba a wancan lokaci, wato ‘ White Paper’ na daga cikin shawarwarin da kwamitin da gwamnatin ta kafa ta bata.
Ranar 30 Ga Nuwamba, 1994 gwamnatin gwamna Lawan Jafaru Isa ta kafa kwamitin sasantawa da yafe wa juna tare da neman shawarar yadda bangarorin biyu za su yi zaman lafiya da lumana da junan su.
Tsohon Gwamnan Kaduna Usman Ma’azu ne Shugaban Kwamiti, tare Shugaban bangaren yankin Zangon Kataf, Atyap na yankin.
Cikin 1995 Kwamitin AVM Usman Mu’azu ya bayyana rahoton sa, tare da sanar da kasa warware wasu manyan matsaloli uku da suka hada da:
Wadanda ke da hakkin mallakar wasu gonaki.
Fitar da Rahoton Cudje, wanda gwamnati Dabo Lere ta yi karkashin mai shari’a Cudjo da kuma batun sakin wadanda aka kulle.
Sake barkewar rikici a yankin Zangon Kataf da Kauru a ranar Alhamis, 11 Ga Yuni, hakan ya sa Gwamnatin Kaduna kafa dokar ta-baci, ba fita a kananan hukumomin Zangon Kataf da Kauri. Musamman ganin cewa barkewar rikicin na da nasaba da rikicin gonakin 1992Umar
Gwamnatin Kaduna ta ce za ta yi dukkan kokarin da za ta yi domin tabbatar da cewa an samu maslahar shawo kan wannan rikici, yadda nan gaba ba zai sake tashi ba.
Ta nuna takaicin tsawon shekaru 28 da afkuwar wancan rikici, amma kuma har yanzu kurwar sa na bibiyar yankin.
Mambobin Kwamiti:
Adamu Mansur (Shugaba) Babban Sakatare Ma’aikatar Jin Dadin Al’umma
Chris Umarh – Babban Sakatare, Ma’aikatar Shari’a
Abdullahi Sani – Babban Sakatare, Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida.
Habiba Shekarau – Babban Sakatare, Ma’aikatar Gidaje
Ibarahim Jere – Babban Sakatare, Ma’aikatar Ayyukan Jama’a
Phoebe Yayi – Babban Sakatare, Ma’aikatar Ma’aikatan Ilimi
Aisha K. Mohammed – Babban Sakatariyar Ma’aikatar Ma’aikatan Gwamnati
Bulus Audu – Maiba Gwamna Shawara.
An ba su makonni shida domin su rika rahoton su.