Ma’aikatar Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta rage tsawon wa’adin shekaru biyu da ake daukar matasa ayyukan N-Power, zuwa kasa da shekaru biyu.
Minista Sadiya Faruq ce ta bayyana haka wurin wani taron musamman da ta yi tare da wasu takwarorin ta ministoci, a ranar Talata a Abuja.
Ta yi wannan taron ganawa ne da Ministan Gona Sabo Nanono, Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Clem Agba, Ministan Lafiya Osagie Ehanire da kuma Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen. Sai kuma Karamin Ministan Ilmi Emeka Ewajuiba.
Sadiya ta ce za a rage yawan shekarun da matasa ke yi a karkashin aikin N-Power, yadda za a kirkiro wasu tsare-tsaren da za a fadada domin amfanar al’umma masu yawa.
Ministar dai ba ta fadi adadin ko shekara daya kacal ko kasa da haka ne za a rika daukar aikin N-Power din ba.
Sai dai ta yi bayani dalla-dalla na sabbin shirye-shiryen da za a kirkiro da kuma rukunin jama’ar da za su ci moriyar shirin.
Daga ciki akwai shirin Inganta rayuwar mata marasa galihu, ta yadda za a koya musu sana’o’in da suka jibinci noma, lafiya da kuma sauran dabarun dogaro da kai
Ministocin sun kuma amince a bullo da shirin yadda za a rika tallafa wa matasa su na cin moriyar ilmin da suka samu bakin gwargwado domin su rika amfani da shi su na kirkirar sana’o’in na dogaro da kai.
Idan ba a manta ba, a farkon wannan makon ne Premium Hausa ta buga labarin cewa Gwamnatin Buhari ta ce ba za ta dauki ma’aikatan N-Power su 200,000 na farkon dauka ta maida su ma’aikatan dindindin na gwamnatin tarayya ba.