Gwamnatin Tarayya ta amince za ta ware zunzurutun kudi har naira bilyan 13 domin sayen maganin feshin farin-dango a jihohi 12 na Arewacin kasar nan.
Ministan Harkokin Noma Sabo Nanono ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Ya ce Gwamnatin Tarayya na sane da illar da farin-dango ke ci gaba da kan yi a Afrika ta Gabas da kuma Gabas ta Tsakiya.
Nanono ya ce za a yi wannan feshin ne domin a hana farin-dango kassara amfanin gonar da ake kokarin nomawa a daminar 2020.
Jihohin da aka ware kudaden domin yaki da farin-dango, sun hada da Kebbi, Sokoto, Zamfara, Katsina, Kano, Jigawa, Bauchi da Gombe.
Akwai kuma jihohin Taraba, Yobe da kuma Barno, duk su na cikin wannan tsari.
Yadda Farin-dango Suka Darkako Afrika Ta Yamma:
Makonni biyu baya, PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa Hukumar Abinci ta Majisar Dinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa farin-dango na daf da mamaye ilahirin gonakin Yankin Afrika ta Yamma, nan da cikin watan Yuni mai kamawa.
FAO ta ce yanzu haka milyoyin farin-dango za su gaba da haihuwa da kyankyashe milyoyin ‘ya’ya a kasashen Ethiopia, Kenya, Sudan, Somalia da yankin Afrika ta Yamma.
“Milyoyin farin-dango na ci gaba da kyankyashe ‘ya’ya su na zugar nausawa Sudan. Abin tsoron shi ne idan suka nausa suka mamaye yankin Sahel na Afrika ta Yamma.”
Darakta Janar na FAO, QU Dongyu ya kara da cewa duk wani kokarin daukar matakan da za a iya yi, zai dauki lokaci kafin aiwatarwa.
Ya ce wannan fargabar ta biyo bayan la’akari da irin barnar da farin-dangon suka yi a Sahel har zuwa yankin Yemen.
Ya ce annonar farin ta samu ne sakamakon ruwan sama mai tarin yawa da aka samu shekaru biyu da suka gabata, inda hakan ya bai wa farin sukunin kyankyashe ‘ya’ya masara iyaka.
Kumanin farin-dango bilyan 200,000 suka mamaye kasar Kenya. Kuma an kiyasta cewa a rana daya sukan iya cinye abincin da mutum milyan 84 za su iya cinyewa.
Farin sun yi mummunar barnar dubban daruruwan hektocin gonaki a Afrika ta Gabas.
Hukumar FOA na fargabar cewa yawan farin zai iya nunkawa sau 500 cikin watan Yuni, su yi yawan da za su iya mamaye amfanin gonakin Afrika ta Yamma baki daya, ko ma a ce kasashe 30.
Tuni dai an fara kokarin kaddamar da gidauniyar talladin dala milyan 311.6 domin a yi wa farin-dangon taron-dangi kisa da maganin kwari.
“Mu na bakin kokarin mu, amma aikin akwai wahala kuma zai iya daukar lokaci, tunda dai farin yawon mamaya su ke yi daga nan su nausa can. Za a dauki watanni kafin a kai ga samun nasara.”
Dongyu ya yi maraba da shirin samar da dala milyan 500 da Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin yi domin yaki da farin-dango a Gabas ta Tsakiya da kuma Afrika.
Daga nan ya yi rokon ci gaba da bayar da gudummawa daga masu bayar da gudummawa a duniya.
Fargabar da ake ci gaba da yi shi ne, yadda a yanzu bilyoyin farin-dangon ke ci gaba da kyankyashe bilyoyin ‘ya’ya. Su kuma wadannan ‘ya’yan, nan da cikin watan Yuni za su yi girman da za su rika cinye shuke-shuke komai yawan su a duk gonakin da suka dira.
Hakan inji rahoton zai kara kawo mummnan matsanancin karancin abinci.
“Abin ya zama bugu biyu. Ga annobar Coronavirus ga kuma annobar farin-dango. Su duka za su kawo bala’in karancin abinci.” Cewar Dongyu.
Farin dango a wani rahoton za su cinye abincin mutum milyan 25 a Afrika ta Gabas, a Yemen za su cinye amfanin gona na abincin mutum milyan 17.