Gwamnatin tarayya ta rage kudin da ke biya don samun katin shaidar yin aure da wanda ake badawa a wuraren ibada.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida
Mohammed Manga ya Sanar da haka ranar Litini a takarda da aka raba wa manema labarai.
Bisa ga Wannan takarda Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ya ce gwamnati ta rage kudin daga Naira 30,000 zuwa 6,000 da za a biya na tsawon shekara biyar.
Bayan haka gwamnati ta rage farashin kudin sabunta katin shaidar aure zuwa Naira 5,000 da za a biya na tsawon shekara uku a maimakon Naira 30,000 da Za a biya a shekara daya.
Daga yanzu ma’aurata za su biya Naira 15,000 maimakon Naira 21,000. Sannan wuraren ibada za su biya naira 25,000 maimakon naira 35,000.
Wannan canji da gwamnati yi zai fara aiki ranar 1 ga watan Yuli.
A shekarar 2019 Gwamnatin Tarayya ta shigo da sabon Lasisin Daura Aure wanda ya kunshi dukkan nau’ukan aurarrakin da ake daurawa a Najeriya.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, Georgina Ehuriah ta ce ma’auratan da ba su mallaki katin shaidar auren su ba, to za su iya bude shafin intanet na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, domin su sabunta lasisin na su.
Ehuriah ta kara da cewa ba dukkan wuraren ibadu ba ne aka amince su daina daura aure ba.
Daga nan sai ta shawarci ‘yan Najeriya su tabbatar da cewa sun daura aure wuraren da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta amince su rika daura aure.