Gwamnati ta raba wa kananan manoma irin cocoa 66,000

0

Gwamnatin Najeriya ta ce ta na aikin raba wa kananan manoma irin cocoa har guda 66,000, domin rage radadin kuncin da zaman dolen da cutar Coronavirus ta sa su.

Karamin Ministan Gona Mustaoha Shehuri ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke kaddanar da shirin rabon irin cocoa din a jihar Oyo.

Ya ce kyauta Gwamnatin Tarayya ke rabon irin cocoa din, sauran kayan tallafin kuma an yi wa manoma ragin tallafi har na kashi 75 bisa 100.

“Wannan ma’aikata kuma ta na raba maganin kwari na sama da yawan nauyin kiligiram 18,000, domin fesa wa tsutsar da ke addabar masara.” Inji Karamin Minista.

Daga nan Shehuri ya yi kira a rika hada guiwatsakanin gwamnatin tarayya, gwamnatin jiha da kuma sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa ba a samu karancin abinci a kasar nan, saboda annobar Coronavirus ba.

Duk da dai mun san akwai kokarin da wasu kungiyoyi da jama’a ke yi masu kishin bunkasa harkar noma, to akwai kuma bukatar gwamnati ta kara zabura wajen tallafa wa manoman da suka jajirce wajen ganin cewa harkar noma ba ta samu tawaya ba.

“Don haka Ma’aikatar Gona tare da Cibiyoyin Bunkasa Harkokin Noma da ke karkashin ta, su nata kokarin binciko hanyoyin Inganta noma domin tabbatar da samun wadatacce kuma ingantaccen abinci a kasar nan.

Minista ya ce Coronavirus babbar annoba ce wacce kisan ta sai dubu ta taru. Don haka ya ce akwai bukatar a kara hobbasa domin a taru a kashe cutar baki daya.

Gwamnan Oyo Oluseye Kehinde, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar ya wakilta, ya ce kasashen da suka rigaya suka tsere a harkar noma,sun yi nassrart hada nomanzamani ne da kuma bunkasa harkar noman, gyara amfanin gona da kuma inganta noman gadan-gadan.

Gwamnati dai ta ce an zabi jihar Oyo domin kaddamar da shirin rabon kayan noman, saboda jiha ce mai cibiyoyin bunkasa noma, kuma ta shahara wajen noman doya da cocoa.

Share.

game da Author