Gwamnatin Tarayya ta karyata wani labari da ta ce ya na yawo a kafafen soshiyal midiya, cewa za ta dauki matasan N-Power kashi na farko (Batch A) ta ba su aiki na dindindin a karkashin gwamnatin tarayya.
Mataimakiyar Darakta Rhoda Iliya, ta Ma’aikatar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a ce ta y wannan karin hasken a Abuja.
Rhoda ta ce ba “gaskiya ba ne bayanan da aka rika watsawa a soshiyal midiya cewa a ranar 12 Ga Yuni, Shugaba Muhammadu Buhari zai yi bayanin daukar matasan ‘N-Power’ na ‘Batch A’ zuwa ma’aikatan gwamnatin tarayya na dindindin.”
Cikin 2016 ne Gwamnatin Tarayya ta dauki matasa 200,000 aikin wucin-gadi na N-Power, ta na biyan kowanen su naira 30,000 a wata.
Sai dai kuma aiki ya samu cikas da tsaiko bayan shekaru biyu, inda biyan kudaden alawus din ya kakare.
Cikin shekarar da gabata ne Shugabar Tsarin N-Power ta lokacin, Maryam Uwais ta shaida wa Premium Times ta wayar tarho cewa Gwamnatin Tarayya ta tuntubi gwamnoni su duba yiwuwar daukar matasan aiki a jihohin da kowanen su ya ke.
Amma kuma cikin 2019, Shugaba Buhari ya dauke aikin N-Power daga Ofishin Maryam Uwais ya maida Ma’aikatar Again, Jinkai da Inganta Rayuwar Jama’a, a karkashin Minista Sadiya Faquk.
N-Power na daya daga cikin Shirin Inganta Rayuwa na Kasa (NSIP) da Gwamnatin Tarayya ta kirkiro cikin 2016, domin rage radadin talauci, samar wa matasa ayyuka da kuma rage gagarimar barazanar matsalar tsaro.