Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa da iyalan sa za su killace kan su na tsawon kwanaki 14 a dalilin samun tabbacin cewa daya daga cikin ‘ya’yan sa ya kamu da cutar Korona.
Babban sakataren yada labaran gwamnan Okowa, Olisa Ifeajika ya sanar da haka a garin Asaba.
“Muna kira ga mutane da su juri saka takunkimin fuska, a rika wanke hannaye da ruwa da sabulu sannan a sai gwamatsuwa cikin mutane domin cutar Korona gaskiya ce kuma tana yaduwa cikin al’ummar mu.
Idan ba a manta ba a ranar 21 ga watan Yuni ne aka bayyana kamuwa da cutar da sakataren gwamnatin jihar Chiedu Ebie da kwamishinan yada labarai na jihar Charles Aniagwu suka yi.
A dalilin haka gwamnati ta yi kira ga mutane a jihar da su kiyaye sharuddan gujewa wa kamuwa da cutar.
Gwamnati ta ce asibitocin jihar na nan na aiki a koda yaushe domin duba wadanda suka kamu da cutar da sauran cututtuka.
Saboda haka gwamnati na kira ga mutane da su gaggauta zuwa asibiti da zaran mutum bashi da lafiya domin a duba shi.
A yanzu dai mutum 715 ne suka kamu da cutar a jihar.
Sannan a kasan gaba daya mutum 22,614 sun kamu, an sallami mutum 7822, mutum 549
sun rasu.