Gwamnan Abia, Ikpeazu ya kamu Korona

0

Gwamnati jihar Abia ta sanar cewa gwamnan jihar Okezie Ikpeazu ya kamu da cutar Covid-19.

Kwamishinan yada labarai John Kalu ya Sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai ranar Litini.

A takardar Kalu ya ce Sakamakon gwajin cutar da aka yi wa Ikpeazu ya nuna gwamnan Yana dauke da kwayoyin cutar.

“A ranar 30 ga watan Mayu gwamnan aka dibi jinin Gwamna Ikpeazu domin yin gwaji. Sai dai a wannan lokaci Sakamakon gwajin ya nuna ba ya dauke da wannan cuta.

“Ranar 2 ga watan Mayu Ikpeazu ya kara aikawa da jinin sa domin ya tabbatar baya dauke da kwayoyin cutar, sai dai kuma a wannan karo sakamakon ya nuna ya kamu da cutar.

Kalu ya bayyana cewa tun kafin sakamakon gwajin ya fito Ikpeazu ya killace kansa a gida sannan ya danka wa mataimakin sa Oko Chukwu ragamar mulkin jihar har sai Allah ya bashi lafiya.

Idan ba a manta a makon da ya gabata Ikpeazu ya umurci duk mambobin kwamitin zantarwar jihar su bada jininsu a Yi musu gwajin cutar bayan an samu daya daga cikin babban jami’in gwamnati ya kamu da cutar.

Sakamakon gwajin cutar da Hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi ya nuna cewa mutum 83 sun kamu da cutar a jihar.

A yanzu haka Ikpeazu shine gwamna na hudu da ya kamu da cutar a kasar nan.

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde.

Share.

game da Author