Gwamantin Buhari za ta sako tubabbun ‘yan Boko Haram 603 su koma gidajen su

0

Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta bayyana cewa nan da watan Yuli ne aka shirya sallamar wasu tubabbun ‘yan Boko Haram su 603 su koma cikin jama’a, su ci gaba da sabuwar rayuwa.

Kakakin Yada Labaran Hedikwatar Tsaro ta Kasa, John Enenche ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce tuni ma aka rigaya aka sallami wasu 280, cikin su har da ‘yan Chadi biyu da aka damka ga jami’an tsaron kasar su, bayan an kammala yaye su daga horon koyon sana’o’in dagaro da kai da ake yi musu.

Enenche ya ce tun cikin 2016 aka fara wannan shiri na karbar tubabbun Boko Haram da suka yi saranda don kan su.

Ya ce an shigar da tubabbu 893 a shirin, an sallami 280, yanzu saura 603 da ake shirin yayewa a sallama nan da watan Yuli.

Tubabbun Boko Haram an rika shigar da su wani shiri ne mai suna DRR, wato Deradicalisation, Rehabilitation da kuma Reintegration.

‘Deradicalisation’: Wato dai ana nufin tattara su a killace a karkashin kulawar sojoji, ana yi musu wankin kwakwslwar kankare musu akidar Boko Haram da ta’addancin da ke tattare da akidar kungiyar.

Ana yin wanan wankin kwakwalwa ne ta hanyar yi musu nasiha, jan-hankali da kuma wa’azi.

‘Rehabilitarion’: A nan kuma ana rika kula da su ne ta hanyar duba lafiyar su, tabbatar da ba su da cututtuka ko tabuwar kwakwalwa sanadiyyar shan kwayoyi da sauran su.

Sai kuma a rika koya musu sana’o’in hannu domin dogaro da kai idan an sallame su sun koma gidajen su.

Ana kuma hada musu da dan tallafi na jarin fara sana’ar dogaro da kai.

‘Reintegration’: Wato tabbatar da cewa sun zama matasa nagari, sun watsar da mummunar akidar kisa da hare-hare da sunan addini. To sai a maida su cikin ‘yan uwa, iyaye ko iyalan su, su ci gaba da gudanar da sabuwar rayuwa.

Enenche ya ce ba gaskiya ba ne kamar yadda wasu ke yarfen cewa wai za su shiga cikin jama’a su ci gaba da shuka ta’addanci.

Ya ce ba kowane dan ta’adda ake yi wa wannan wankin kwakwalwa ba, sai wanda ya tuba don kan sa, ya yi saranda ga jami’an tsaro.

Ya kara da cewa wannan tsari kuwa ba Najeriya ce ta fara shi ba. Duk duniya an amince da irin sa, matsawar wanda ke fitinar al’umma ta tuba, ya ajiye makamai, to sharuddan Dokokin ‘Yancin Dan Adam na Duniya sun ce a sake karbar sa a maida shi cikin al’umma, bayan an sake dora shi a kan hanya madaidaiciya.

A karshe ya ce akwai ma’aikatan da ke aiki a karkashin wannan tsari su 468 daga kungiyoyi 17.

Ya kara da cewa wannan ma wata hikima ce ta kokarin kawar da ta’addanci a kasar nan.

Share.

game da Author