GOGUWAR KOMAWA PDP: Mataimakin gwamnar jihar Ondo ya koma PDP

0

A ‘yan kwanakin nan an yi ta kai ruwa rana tsakanin gwamnan jihar Ondo Akeredolu da mataimakin sa Agboola Ajayi da ya kai ga har motocin sa na fita an rika yi wa Ajayi iya ka da su a fadar gwamnati.

Mataimakin gwamna Ajayi ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa PDP a ranar Lahadi bayan wata takaddama da su kayi da sufeto janar din ‘yan sandan jihar a fadar gwamnati dake Akure.

A ranar lahadi, an ruwaito yadda sufeto janar din ‘yan sandan jihar, ya hana mataimakin gwamna Ajayi yin fita da motocin alfarma da yake amfani da sannan ya garkame sa a fadar gwamnati.

Daga baya dai mataimakin gwamna Ajayi ya tattara nas-ina sa ya garzaya mazabarsa ya yanki tikitin komawa jam’iyyar PDP.

Zaben jihar Edo da Ondo ya gabato matuka. Wannan canja sheka da mataimakin gwamnan jihar yayi zai kawo wa jihar Edo cikas matuka idan bata maida hankali ba.

A jihar Edo ma, gwamnan ne kacokan ya waske daga APC ya koma PDP abinsa batan tirnukewar rikici da yaki ci yaki cinyewa tsakanin sa da dakataccen shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole.

Tuni dai har jam’iyyar PDP ta bashi damar yayi takarar fidda gwani a inuwar jam’iyyar da ake ganin shine zai yi nasara a zaben idan anyi a wannan mako da aka shiga.

Share.

game da Author