Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta bada gudunmawar dala biliyan 1.6 domin tallafa wa kamfanin sarrafa magunguna, Gavi don yin magungunan rigakafi.
Gates ta bayyana haka ne ranar Juma’a a taron da gwamnatin kasar UK ta shirya domin samar da isassun maganin rigakafi wa mutane musamman a kasashen masu tasowa.
Shugabanin kasashen duniya da dama sun halarci taron sannan sun bada nasu gudunmawar wa asusun Gavi.
Kafin a kammala taron asusun Gavi ta tara jimlar dala biliyan 8.8.
Bill Gates,wanda shine shugaban gidauniyar ya bayyana cewa Gavi Za ta yi amfani da wadannan kudade ne domin sarrafa maganin rigakafi da Za a ci gaba da yi wa yara allurar rigakafi a duniya.
Sakamakon bincike da aka fitar a shekarar 2018 ya nuna cewa yaro daya cikin yara 10 bai gama yin allurar rigakafi ba ko kuma ba su taba yin allurar rigakafi ba a kasashe masu tasowa.
Kamfanin Gavi ta dade tana aiki da gwamnatocin kasashen da suka ci gaba, kungiyoyin kiwon lafiya domin sarrafa da samar da maganin rigakafi wa kasashen masu tasowa.
Wannan aiki da kamfanin ke yi ya taimaka wajen samar da allurar rigakafi da za a yi wa yara da hakan zai taimaka, wajen rage yawan mace-macen yara kananan daga cututtuka musamman a orin wadannan kasashe.