Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta bayyana damke wani fasto mai suna Inimfon Eyo, bayan ya boye wasu ‘yan mata 8 masu kananan shekaru cikin wani gida, har ya yi wa daya daga cikin su fyade.
Wadda aka yi wa fyaden dai ‘yar shekara 15 ce, sauran ‘yan matan ma daga shekaru 13 suka kama zuwa 16.
Kwamishinan ‘Yam Sandan Akwai Ibom Imohimi Edgal, ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba a Uyo, babban birnin jihar cewa faston ya tara ‘yan matan a cikin gida ne da nufin cire musu kurwar da ke hana musu nasibi a rayuwa da korar musu shaidanun da ke kan su.
An damke faston a ranar 18 Ga Yuni kan titin Nung Atim, cikin birnin Uyo.
“An kuma kama wasu mutane 11 a jihar daban-daban, wadanda aka samu da aikata laifin fyade, cikin su har da wani mai suna Akpan Kingsley, wanda ya shafe tsawon lokaci ya na yi wa ‘yar sa mai shekaru 14 fyade.
“Kuma akwai wani da aka kama, mai suna Sunday Ime, a Karamar Hukumar Esit Emit, shi ma wata ‘yar sa mai shekaru 16 ya shafe shekara daya cur ya na yi wa fyade.
“Da farko bayan abin ya dame ta, ‘yar ta gudu zuwa gidan wata ‘yar uwar ta. Amma daga baya ta koma gida, shi kuma uban ya ci gaba da yin lalata da ita..
“An kuma kama wani mai suna Etebong Monday Harrison, wanda ya yi lalata da karamar yarinya ‘yar shekara biyar.”
Kwamishinan ‘yan sanda ya ce saboda yawaitar fyaden kananan yara da ake yi a jihar, an hana iyaye dora wa kananan yara talla.
“Za mu kama iyayen duk da suka dora wa kananan ‘ya’yan su talla, domin kotu ta hukunta su, kamar yadda doka ta tanadar.”