Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu, ya bayyana cewa Hukumar sa za ta yi dirar-mikiya a kan ‘yan Najeriya da suka saci kudi suka boye a Ghana.
Da ya ke magana ranar Juma’a a Abuja, ya ce EFCC na nan ta na hada dukkan karfin bayanan da suka wajaba domin ta fara bin su ta na damkewa, tare da dawo da makudan kudaden da suka sata suka boye a can kasar.
Magu ya yi wannan bayani ne lokacin da tawagar Cibiyar Sanin Makamar Tattalin Kudade da Siyasa (CIPRMP) ta kai masa ziyasa a hedikwatar EFCC, a Abuja.
Magu ya ce EFCC ta hada kai da takwarar ta da ke kasar Ghana, domin aikin kwato wadannan makudan kudade.
Ya ce zamba da cin hanci da rashawa manyan illoli ne da ke karya tattalin arziki.
Don haka sai Magu ya yi kira, “ga duk wanda ya san yadda aka tabka wata gagarimar sata ko wurin da aka kimshe kudaden sata, to ya sanar wa EFCC.
“Akwai garken ’yan Najeriya da suka saci makudan kudade suka boye a Ghana. Za mu je mu dawo da kudaden da suka sace da kadarorin da suka saya da kudin sata, duk za mu kwato su zuwa Najeriya.” Inji Magu.
Ya kuma yi kira da ‘yan Najeriya su yi watsi da yarfe da bakin fentin da ake goga masa. Ya na mai cewa EFCC a karkashin sa ba ta wata kumbiya-kumbiya, komai a fili ta ke gudanar da shi.
Discussion about this post