DUMI-DUMI: Ana can ana gumurzun yaki tsakanin Boko Haram da sojoji da garin Monguno

0

Rahotanni sahihai sun tabbatar wa Premium Times cewa yanzu haka ana can ana barin wuta tsakanin Boko Haram, bangaren ISWAP a garin Monguno cikin jihar Barno.

Maharan dai sun yi wa garin dirar-farin-dango, suka rika bude wuta ta ko’ina.

Monguno can ne mahaifar tsohon Janar na soja, Ali Monguno, kuma Mashawarcin Buhari a Fannin Tsaro.

Akwai akalla ‘yan gudun hijira 120 a garin.

Monguno na kilomita 93 daga Gubio, inda Boko Haram suka kashe mutum 81 a farkon makon jiya.

Wani jami’in CJTF mai suna Bunu Malam, ya tabbatar da hakan kuma ya ce an sanar da su halin da garin ya ke ciki lokacin da aka fara gumurzun wajen 12 na rana. Amma dai a yanzu ba a iya sanin halin da garin ke ciki.

Share.

game da Author