Duk da gargadin da Buhari ya yi kada a je Kotu, Korarrun mambobin kwamitin gudanarwar APC sun ce za su garzaya kotu

0

Duk da gargadin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi cewa kada ‘yan jam’iyyar su rika kai jam’iyyar kotu, yana mai cewa jam’iyyar za ata rika daukar mataki akai da hukunta ‘yan jam’iyyar Korarrun mambobin jam’iyyar APC sun sha alwashin garzaya wa kotu don kalubalantar matsayar da kwamitin zartaswar jam’iyyar ta dauka da yayi sanadiyyar korar su daga mukaman su kaf daga APC.

Jagorar wadanda aka kora su 18 Hilliard Eta ya ce tun farko mataimakin sakataren jam’iyyar, Victor Giadom ba shi da damar kirar zaman kwamitin zartaswar jam’iyyar wanda Shugaba Buhari ya amince da shugabncin sa kuma ya halarta.

Sunce matsayar da kwamitin zartaswar jam’iyyar ta dauka bai yi daidai da dokar jam’iyyar ba. Ta yanko wasu sassa na dokar jam’iyyar da ya rusa duk abinda ya gudana ranar Alhamis da ya haramta musu ci gaba da nuna kansa mambobin kwamitin NWC.

Korarrun ‘yan jam’iyyar sun ce zasu tattauna da Lauyoyin su domin yiwuwar dira kotu kalubalantar korarsu da a kayi.

Yadda aka yi wa Tinubu taron dangi

Yunkuri, kokari, gaganiya da muradin tsohon gwamnan jihar Lagos Bola Tinubu na gadon kujerar shugaban kasa daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari a 2023, ya samu cikas da koma-baya, ganin yadda a rikicin da ya dabaibaye APC, Buhari ya goyi bangaren masu tsantsar adawa da Tinubu.

Tinubu dai shi ne bangon jinginar Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole da aka dakatar. Kuma da shi din ne Oshiomhole ke tinkaho.

Tinubun da ‘yan APC ke kira “Jagoran Jam’iyya na Kasa”, ya ta taka muhimmiyar rawa wajen kafa jam’iyyar APC da kuma nasarar da ta samu a zaben shugaban kasa na 2015.

Duk da dai Tinubu bai fito ya bayyana muradin sa a fili ba, amma dai a fili ta ke cewa ana rade-radin ya na ta mafarkin zama shugaban kasa a 2023, bayan wa’adin Buhari na zango na biyu kuma na karshe ya kare a ranar 29 Ga Mayu, 2023.

A ranar Laraba Buhari ya fito baro-baro ya bayyana cewa ya na goyon bayan bangaren shugabancin riko na Victor Giadom.

Giadom ya yi amfani da umarni da hukuncin kotu ne ya ce shi ne shugaban riko na kasa na APC, bayan da kotu ta tabbatar da dakatarwar da aka yi wa Tinubu.

Su kuwa wasu mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) na APC, su 18, sai suka bayyana a ranar waccan Talata cewa sun nada Mataimakin Shugaba na Kasa da ke Shiyyar Kudu, Abiola Ajimobi, a matsayin Shugaban Riko.

Ranar Litinin kuma sai NWC din dai suka sauke Victor Giadom daga mukamin sa, suka nada Worgu Boms a madadin sa.

Sai dai kuma a cikin wata sanarwa daga hannun Kakakin Yada Labaran sa Garba Shehu, Shugaba Buhari ya ce shi dai ya na bayan Victor Giadom, domin shi ne hannun da doka ta nuna da yatsa a matsayin wanda ya dace a bi.

Su kuwa ‘yan bangaren Ajimobi, sai suka rika cewa taron Kwamitin Zartaswa da Giadom ya kira wanda Buhari ya ce zai halarta, haramtacce ne. Har ma suka rika jawo wasu ayoyin da suka ce sun haramta taron daga cikin kundin dokokin Najeriya.

Sakataren APC na Kasa Waziri Bulama, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa taron da Giadom ya kira ya kauce wa dokar jam’iyyar APC.

Share.

game da Author