A alkaluman da hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i ta kasa, JAMB ta fitar sun nuna cewa duk da fama da hare-haren Boko Haram, jami’ar Maiduguri ta fi kowacce jami’a daukan dalibai a 2019.
Wannan abu ya yi matukar ba mutane mamaki ganin cewa har yanzu jihar na fama da Boko Haram da tashin hankali.
A shekarar 2019, jami’ar ce tafi daukan dalibai cikin duka jami’o’in Najeriya.
A 2019, jami’ar Maiduguri ta dauki dalibai 12,523 kari akan 11,665 da suka shiga jami’ar a shekarar baya.
Darektan yada labaran jami’ar Ahmed Mohammed ya shaida cewa an samu karin yawan dalibai dake son yin karatu a jami’ar ne saboda tsaro da jami’ar ta sa.
” Baya ga tsaro da aka saka na jami’an sojoji, ita kanta jami’ar ta kafa nata jami’an tsaron na ‘yan banga da masus farauta domin samar da tsaro a makarantar.
” Sannan kuma idan baka da shaidar ko kai wanene ba za a barka ka shiga jami’ar ba.
Jami’o’i 10 da dalibai suka fi samun gurbin karatu a Najeriya a 2019
1 – Jami’ar Maiduguri ta ba dalibai 12,435 guraban karatu a jami’ar.
2 – Jami’ar Calabar – 12,237
3 – Jami’ar Benin – 11,747
4 – Jami’ar Ilori – 11,616
5 – Jami’ar Legas – 9,625
6 – Jami’ar Fatakwal – 9,107.
7 – Jami’ar Nnamdi Azikwe ta ba daliba 8,880 guraban karatu
8 – Jami’ar Najeriya, Nsuka,8,585
9 – Jami’ar Jihar Ekiti, EKSU, 8,119
10 – Jami’ar Jihar Ribas, RSU, taba dalibai 7,843 guraban karatu.
Kwalejojin Kimiyya da Fasaha
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna wato, Kaduna Poly ta fi ba dalibai guraban karatu mafi yawa a 2019.
Ga jerin kwalejojin
Kaduna Polytechnic, Kaduna — 7,897
Yaba Tech, Yaba, Legas — 4,046
The Polytechnic, Ibadan, Oyo — 3,270
Akanu Ibiam, Unwana, Ebonyi — 3,212
Polytechnic mallakin jihar Filato dake Barkin-Ladi — 3,024
Polytechnic mallakin jihar Legas dake , Ikorodu — 2,822
Federal Polytechnic, Offa, Kwara — 2,711
Federal Polytechnic, Ilaro — 2,646
Ogun State Institute of Tech (formerly Gateway ICT Poly), Igbesa — 2,471
Federal Polytechnic, Ado-Ekiti — 2,432
Kwalejojin koyan aikin malunta
1 – Federal College of Education, Pankshin, Plateau — 4,828
2 – Federal College of Education, Kano — 4,793
3 – Federal College of Education (Technology), Gombe — 4,720
4 – Kaduna State College of Education, Gidan-Waya — 4,276
5 – Federal College of Education, Zaria — 4,188
6 – College of Education, Akwanga, Nasarawa — 2,923
7 – Federal College of Education (Special), Oyo — 2,771
8 – Isa Kaita College of Education, Dutsin-Ma, Katsina — 2,735
9 – Federal College of Education (Technology), Potiskum, Yobe — 2,650
10 – Federal College of Education, Osiele, Abeokuta — 2,638