Tashin farko dai kada ma wani ya yi tunanin ko mai wannan rubutun bai yarda akwai cutar Coronavirus ba. Na yarda akwai ta, kuma wata uku kenan cur ina takure a wuri daya, a cikin yanayi na kaffa-kaffar gudun kamuwa da wannan cutar.
Cutar da ta kashe dubun-dubatar Turawa da Amurkawa sama da dubu 80,000 ai duk mai hankali ya san abin tsoro ce.
Amma maganar gaskiya, matakan da Gwamnatin Tarayya ta dauka kuma ta ke dauka wajen yaki da cutar Coronavirus, dodorido ne kuma duk an shafe watanni uku a takure, a karshe talaka aka kuntatawa, shi da bai ma san ta yadda aka yi masu hali da wasu masu mulki a kasar nan suka fita kasashen waje, suka jajibo masa wannan alakakai, wai ita cutar Coronavirus ba.
Gwamnatin Tarayya ta bi ta firgita kasar nan kakaf, an nuna wa jama’a tamkar Coronavirus ta fi mutuwa ita kan ta tashin hankali.
1. Ya za a ce an kulle kasar nan kakaf, an hana kowa motsawa, da dama sun mutu saboda kasa samun kulawa a asitoci. Milyoyi sun yi asarar bilyoyin kudade. Dubban ‘yan Najeriya sun rasa aikin yi. An hana mutane fita a lokacin da mutanen da suka kamu a kasar nan ba su kai mutum 80.
2. Yanzu kuma tamkar Gwamnatin Tarayya ta gaji da yaki da cutar, ta bar mu a hannun Gwamnonin Jihohi. Su kuma sun sake mu, an ce kowa ya fito a lokacin da cutar ta fi kowane lokaci fantsama a kasar nan.
3. An kulle jama’a a gida. An ce an raba bilyoyin kudade na tallafin rage kuncin radadin talaucin zama wuri daya. Amma kuma duk wanda ka tambaya sai ya ce maka a radiyo ko a soshiyal midiya kadai ya ji an raba kayan agajin.
A Kano an ce an kawo tirela 110 ta kayan abinci. Ban ce ba a raba ba. Amma dai ni dai har yau ban gani ko ji wani ya fito a Facebook ko WhatsApp ya na nuna godiya ko hotunan rabon kayan agajin da aka yi a unguwar su ba.
3. An bi an tayar mana da hankali a kan Coronavirus. Har yau ba ta kashe mutum 400 a alkaluman Hukumar NCDC ba. An bi an ware wa wanann cuta makudan kudaden da ko cikin teku aka watsa su, sai ruwa ya sha su har ya rage.
Amma kuma an yi watsi da mutane karkara a yankuna an bar su a hannun ‘yan bindiga su na yi musu kisan-miyashin da ko a lokacin ‘yan samame kafin zuwan Turawa ba a yi wa mazauna karkara irin wanann kisan wulakanci ba.
4. An sa dan makulli an bude kofar ‘lockdown’, an ce a fita kasuwa, kada a shiga masallaci. Wane bayani za ku yi wa talaka har ku gamsar da shi?
5. An dawo an ce a’a, a shiga masallaci, amma kada a bude kasuwanni. A dai fita a yi harkoki. Shin kasa da takin da dabbobi ake so talakawa su ci ne?
6. Yanzu da gwamnati ta ce kowa ya fito, ta sa ta fisshe shi, shin an gama yaki an ci galaba kan Coronavirus? Raguwa ta ke yi ko karuwa ta ke yi?
7. Me ya sa dukkan matakan da gwamnati ta dauka a kan talakawa kuncin ya yada zango? Ai ma’aikatan Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi wata uku suka shafe zaune dirshan a gida. Amma duk karshen wata ana biyan su albashi.
Shin shi talakan da ba ya daukar albashi ta yaya tallafin bilyoyin kudaden da aka ce an ware za su isa gare shi.
8. Ko gwamnati ta yarda, ko kada ta yarda, kai kada ma Allah ya sa ta yarda. Amma dai ta sani cewa babu wani talakan da zai gamsu da cewa an raba wa dalibai abinci a lokacin da kowane dalibi ke zaune a gidan iyayen sa.
10. An shafe watanni uku cur ana kashe makudan bilyoyi wajen yaki da Coronavirus. A karshe an saki jama’a daidai lokacin da cutar ta fi mamaye kasar nan.
Shin kowa ya yi ta kan sa kenan, ko kuwa kowa ta sa ta fisshe shi?
11. Inda abin ya fi ciwo shi ne, duk da zaman gidan da aka tilasta al’umma tsawon wata uku, duk da makudan kudaden da aka kashe, a karshe an yi an dawo an saki mutane sun fito, ba tare da ce sun gode ba.
Daga masu cewa an takura musu, sai masu cewa Coronavirus dodorido ce, sai kuma masu neman ganin wadanda za su iya kafa shaida da su cewa sun ga ‘alat’ na tallafin Coronavirus a asusun bankunan su.