Shugaban kwamitin dakile yaɗuwar Korona a Najeriya, kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana wasu dalilai da ya sa aka samu raguwar mutuwar mutane daga Korona a Najeriya.
” Da farko dai hakan ya yiwune a dalili samun wadanda je da karancin shekaru ne ke kamuwa da cutar. Akalla kashi 80% da suka kamu da Korona a Najeriya, matasa ne ‘yan shekara 31 zuwa 40. Wadannan shekaru kuwa garkuwar jikin su na da karfin da yake iya dagargaza kwayoyin cutar a jiki.
Ya ce matasa masu karancin shekaru ba su kaiwa da har su rasa rayukan su. Ba kamar sauran kashi 20% din da tsoffi ne ba wasu kuma ma suna fama da manyan cutuka a jikin su.
Ya ce kwamitin sa ta ba da shawarar garkame kananan hukumomin da cutar ta yi wa hawan kawara, domin a samu a iya yi wa mutane gwaji da kula da su yadda ya kamata.
Sauran gari kuma sai dai a ci gaba da bin umarni da dokokin da aka saka domin kauce wa kamuwa da cutar.
Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 490 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum – 118, Delta – 84, Ebonyi – 68, FCT – 56, Plateau – 39, Edo – 29, Katsina – 21, Imo – 13, Ondo – 12, Adamawa – 11, Osun – 8, Ogun – 8, Rivers – 6, Kano – 5, Enugu – 3, Bauchi – 3, Akwa Ibom – 3, Kogi – 1, Oyo- 1 da Bayelsa – 1.
Yanzu mutum 24, 567 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 9,007 sun warke, 565 sun rasu.