Dalilin da ya sa Kotu ta warware auren Abdullahi da Toyin bayan shekara 10

0

Kotu a Ado Ekiti jihar Ekiti ta warware auren shekara 10 dake tsakanin Ibrahim Abdullahi da matar sa Toyin.

A zaman da kotun ta yi ranar 17 ga watan Maris wadannan ma’aurata sun bayyana wa kotu matsalolin da suke fama da su a zaman auren su.

Kotun ta warware kullin auren bisa ga matsalolin da suka bada wanda suka hada da rashin girmama miji, yawan fada da yawan fita da matar take yi da da dare.

Abdullahi ya ce matarsa Toyin ba ta girmama shi, sam bata yi masa ganin shine mijin ta sannan tana yawan fita da dare da bai san inda take zuwa ba. Wani abin ma bata kula da ‘ya’yan su yadda ya kamata.

” Wata rana da muka yi fada Toyin cikin fushi ta dauki wuka tana neman aika ni lahira, Allah dai ya bani sa’ar kwace wukar. Sannan kuma ‘ya’yan mu na zama cikin kazanta babu tsafta.

Sai dai kuma ita mai dakin Abdullahi, Toyin ta musanta dukka abin da mijinta ya fadi wa alkali, ta ce shirga masa karya kawai ta yi.

Toyin ta ce takan fita da dare ne domin ziyartar wata ‘yar uwarta da take da matsala da mijinta.

A karshe dai Alkalin kotun Olayinka Akomolede ta raba auren kuma ta ba toyin,’ya’yan biyu domin ci gaba da kula da su.

Akomolede ta ce Abdullahi zai nema musu gidan hayanda za su zauna kuma zai rika biya musu kudin makaranta.

Share.

game da Author