Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa mafi yawan masu cutar Coronavirus babu wata alama a jikin su mai nuna su na dauke da ciwon.
“Kashi 80 bisa 100 na masu dauke da cutar Coronavirus a kasar nan, babu alamar da ke nuna cutar a jikin sun.
“Dalili kenan akwai wahalar gaske mu gamsar da su cewa akwai cutar a jikin su.
“Ko ka yi kokarin nuna musu ba za su amince da kai ba.Saboda su na jin garau a jikin su, amma kuma a talbijin su na ganin yadda ake nuno masu cutar ranga-ranga. Kuma su na ganin irin yadda suke mutu-kwakwai-rai-kwakawai a Cibiyoyin Kula da Masu Cutar.
“Wasu kuma da sun ji su na da cutar, ba su jira a killace su sai kawai su ko su boye, a neme su a rasa. Da yawa su na guje wa killacewa. Rahotanni da dama daga jihohi sun tabbatar da wasu kuma sun tsere daga inda ake killace da su.” Inji Ehanire.
Da dama sun tsere a Kano, Lagos, Gombe da sauran jihohi da yawa.
Wani likita Mai suna John Oghenehero, ya ce mutane na gudun killacewa ce saboda gani suke yo kamar an yo wa rayuwar su wani bakin tambari.