Dakarun Sojin Najeriya sun darkaki mahara, sun kwato makamai a Zamfara

0

Kodinatan yada labaran rundunar Sojin Najeriya John Enenche, ya bayyana cewa dakarun Najeriya sun damke wani mai safarar bindigogi da harsashai wa ‘yan ta’adda a dazukan Zamfara da Katsina a wani harin kwantar bauna da Sojoji suka yi.

Enenche ya ce bayan haka kuma Sojoji sun dira har wasu daga cikin maboyan maharan dake dajin Zamfara inda suka kama wasu kuma suka kashe wasu. Sannan sun kwato makamai da suka hada da bindigogi kirar adaka da na zamani, harsashai da babura.

” A ranar 5 ga Juni, a cafke wani mai safarar makamai a garin Mararraba Maigora, dake Karamar Hukumar Faskari, jihar Katsina.

” An cafke wasu’yan bindiga uku, an kashe hudu a harin kwantar baunar da Sojoji suka kai maboyar su a kauyukan Yauyau da Zandam.

” Sojoji sun fatattaki wasu mahara da suka arce suka bar bindigogin su kirar adaka da babura hudu da aka kwaso a Dunya-Dangeza. Sannan Sojoji sun ragargaza maboyar wani kasurgumin dan bindiga da aka fi sani da Dan Jangeru a Zamfara.

A karshe rundunar ta roki mazauna kauyuka su rika ba Jami’an tsaro hadin kai wajen samar musu da bayanan sirri a kowanni lokaci.

Share.

game da Author