Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 241 da suka kamu da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Talata.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Asabar, sun nuna cewa Jihar Legas ta samu karin mutum 142, Oyo-15, FCT-13, Kano-12, Edo-11
Delta-10, Kaduna -9, Rivers-9, Borno-8, Jigawa-4, Gombe-3, Plateau-3, Osun-1, Bauchi-1.
Yanzu mutum 10819 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 3239 sun warke, 314 sun mutu.
Duk da yawan mutane da ake samu sun kamu da cutar a kullum a Najeriya, wasu da dama na ganin har yanzu ba a yi wa mutane gwajin cutar yadda ya kamata a kasar.
Jihar Legas na ci gaba da samun daruruwan mutanen da suka kamu da cutar Korona babu kakkautawa.
A ranar Talata kawai, jihar Legas ta samu karin mutum sama da sama da 142 da ya ninka jimlar yawan sauran jihohi 13 da suka samu karin wadanda suka kamu. Akalla jihohi 14 sun samu karin mutanen da suka kamu da kwayoyin cutar a ranar Talata.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum 5, 277 cases, followed by Kano – 970, FCT – 687, Katsina – 371, Edo – 336, Oyo – 327, Kaduna – 297, Borno – 296, Ogun – 280, Jigawa – 274,, Bauchi – 241, Rivers – 248, Gombe – 164, Sokoto – 116, Kwara – 111, Plateau – 108, Delta – 98, Nasarawa – 80, Zamfara – 76, Yobe – 52, Akwa Ibom – 45, Osun – 46, Adamawa – 42, Ebonyi – 40, Imo – 39, Niger – 33, Kebbi – 33, Ondo – 28, Bayelsa – 21, Ekiti – 20, Enugu – 18 Taraba – 18, Abia–15, Anambra – 11, Benue – 9 da Kogi – 2.