CORONAVIRUS: Gwamnatin Legas ta ki bude masallatai da coci-cocin jihar

0

Gwamnatin Jihar Legas ta bayyana cewa duk da gwamnatin tarayya ta bada umarnin bude wuraren ibada, ita ba za ta yi azarbabin bude masallatai, coci-coci da sauran wuraren ibadu a jihar ba.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Anofiu Elegushi ne ya bayyana haka a ranar Talata.

Ya ce Jihar Lagos ba za ta yi gaggawa wajen sake bude wuraren ibada ba, saboda Lagos ce jihar da cutar Coronavirus ta fk yi wa illa a kasar nan.

Ya ce tun ma kafin Gwamnatin Tarayya ta sanar da umarnin bude wuraren ibada a ranar 1 Ga Yuni, jihar Lagos ta yi taron tattaunawa da shugabannin bangarorin addinai domin a ga ko akwai yuwuwar sake bude wuraren ibada.

“A taron da muka yi da limaman masallatai da na coci-coci, mun duba, mun kuma yi nazari, a karshe mu ka ga cewa batun ma a bude wuraren ibadun a yanzu bai taso ba tukunna.

“Limamai sun shaida mana cewa ba za su iya rufe kofar masallaci ba su ce sai mutum 20 kadai ko 50 aka yarda su yi sahun sallah ba.

“Wani limami ma ce mana ya yi, ai daga likacin da ya tayar da sallah, ba zai iya gane ko mamu nawa za su shigo cikin masallaci su yi shi sallah ba, tunda ba waiwayawa zai rika yi ya na kirgawa ba.”

Ya ce daga nan su kan su limaman suka amince cewa lokacin sake bude masallatai bai yi ba tukunna, idan aka yi la’akari da yadda a kullum ake samun dimbin mutanen da ke kamuwa da cutar Coronavirus a Lagos.

A karshe ya ce gwamna ne zai fito da wani sabon umarni idan lokacin da ake ganin ta ya fi dacewa a bude wuraren ibadun ya yi.

Haka kuma ita ma takwarar ta jihar Kaduna, ta bada sanarwar cewa ba ta bada umarnin a bude masallatai da coci-coci ba.

Share.

game da Author