CORONAVIRUS: Dalilin dage ranar fara zirga-zirgar jiragen sama gadan-gadan a kasar nan – Gwamnatin Tarayya

0

Babban Daraktan Kula Da Hukumar Zirga-zirgar Sufurin Jiragen Sama Ta Kasa (NCAA) Musa Nuhu, ya bayyana cewa an dage ranar bude zirga-zirgar jiragen sama a filayen jirage biyar da aka bayyana za a fara kwanan nan, saboda dalilai na rashin kammala shirye-shirye

Ya ce kamfanoni da hukumar tashoshin jirage ba su kammala shirye-shiryen da suka wajaba a tabbatar sun kammala ba, kafin a sake bude zirga-zirgar jiragen a kasar nan.

“Har yau bangaren hada-hadar sufurin jiragen sama a kasar nan, ba su farka sun rungumi gaskiyar abin da ya wajaba su yi wajen fara zirga-zirgar jama’a, ta yadda za a kauce wa kamuwa da cutar Coronavirus ba.”

Najeriya ta rufe filayen jiragen saman ta gaba days cikin watan Maris, bayan barkewar cutar Coronavirus a duniya.

Ya zuwa yanzu cutar ta kashe sama da mutum 400 a Najeriya.

Kwamitin Dakile Cutar Coronavirus ya bayyana cewa za a fara zirga-zirgar jiragen sama a ranar 21 ga Yuni.

Sai dai kuma a yanzu Nuhu ya ce hakan ba zai yiwu ba, saboda ba a kammala shiryawa ba.

Ya ce da muguwar rawa, gwamma kin tashi. Kamata ya yi a bari sai an kimtsa sosai tukunna.

Nuhu, wanda shi ne ya wakilci Ministan Sufurin Jirage, Hadi Sirika, ya ce ganganci ne babba idan aka sake bude tashishin jiragen sama a yanzu.

“Mu na gudun kada jiragen sama su koma jiragen jigilar cutar Coronavirus, maimakon jigilar fasinjoji.” Inji shi.

Ya ce su na sane da yadda jama’a su ka kagara a fara zirga-zirgar jiragen sama, domin su ci gaba da gudanar da harkokin su. To amma dole mu yi taka-tsantsan a matsayin mu na gwamnati, kada garin gyaran doro mu karya kwankwaso gaba daya.”

Share.

game da Author