Chelsea ta lallasa Man City a Landan

0

Kungiyar kwallon kafa ta ManCity ta sha kayi a hannun Chelsea a Birnin Landan a wasan give raini da aka yi ranar Alhamis.

An tashi wasa Chelsea ta jefa kwallaye biyu a ragar Manchester City.

Dan wasan Chelsea, Kevin De Brune me ya rama kwallon farko da Pullicis ya jefa a ragar Manchester City.

A daidai minti 77 kuma sai Dan wasan Manchester City Fenandinho ya tare kwallo da hannu a kusa da ragar su.

Nan take kuwa alkalin wasa ya hura bugun daga Kai sai gola kuma ya lika was Dan wasan Jan Kati.

Dan wasan Chelsea, William bai yi wata-wata ba ya ko doka ta cikin ragar Man City. Kwallo dai ya yi dama shi kuma mai tsaron gida Manchester City ya cilla hagu kwallo kuwa yayi ta kararrawa a raga.

Wannan nasara ba zata da Chelsea ta yi ya na da matukar mahimmanci ga samun shiga Champions league.

Hakan ita ma kungiyar Arsenal ta lallasa Southampton da ci biyu ba ko daya.

Arsenal ta farfado daga suman da ta yi a makonnin wasannin da kowa sai ragargazar ta take yi.

Wannan nasara da ta yi ya na da matukar mahimmanci a gareta duk da bata kusa da wadanda za su samu shiga Champions league.

Share.

game da Author