Buhari ya nada Umar Danbatta shugaban NCC a karo na biyu

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Umar Danbatta shugaban Hukumar NCC ta kasa a karo na biyu.

Kakakin ministan Sadarwa, Ali Pantami, Uwa suleiman ta bayyana haka ranar Juma’a.

Uwa ta ce shugaba Buhari ya amince da nadin Danbatta ne bayan mika sunansa da minisa Pantami yayi domin a sake nada shi a kujerar wannan ma’aikata.

Buhari ya nada Danbatta a karon farko shekaru da suka wuce.

A karshe Pantami yayi wa Danbatta fatan alheri da kuma yin kira a garesa da ya ci gaba da aikin inganta hukumar kamar yadda yake yi a baya.

Umar Danbatta, farfesa ne a harkar fasaha da kimyyar sadarwa.

Share.

game da Author