Buhari ya “girgiza” da kisan kiyashin da aka yi a Gubio, ya umarci Sojoji su ceto wadanda aka sace

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi tir da mummunar harin kisan kiyashin da aka yi a kauyen Gubio dake jihar Barno da aka kashe akalla mutum 81.

Buhari ya ce wannan kisa da Boko Haram bangaren ISWAP suka kai wa mutanen kauyen Gubio ya girgiza shi matuka, ya kuma umarci dakarun Sojin Najeriya su gaggauta ceto wadanda aka yi garkuwa da su day shanun da aka sace.

Wannan mummunar kisan kiyashi da aka yi wa mutane kauyen Gubio ya zo kwanaki kadan bayan babban Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya ziyarci fadan shugaban kasa inda ya shaida wa shugaba Buhari cewa dakarun Najeriya sun kusa gamawa da Boko Haram karkaf.

Shugaba Buhari ya ce yana sauraren cikakken bayanin abinda ya faru daga gwamnan jihar Barno Babagana Zulum bayan ya Gam ziyarar wadannan wurare.

A karshe ya umarci Sojoji su fantsama dajin Sambisa domin bin sawun wadannan ‘Yan ta’adda, su ceto mutanen da suka tafi da su da kuma shanun da suka sace.

Karanta labarin mu na baya:

Wani mazaunin kauyen Gubio ya shaida yadda Boko Haram suka afka musu suka yi ta kashe-kashe tun karfe 10 na safe zuwa hudu na yamma, sannan suka arce da hakimin garin da wasu mutum 7.

Gwamnan jihar Barno Babagana Zulum ya garzaya wannan kauye na Gubio bayan samun labarin wannan hari da aka kai kauyen.

A garin an tabbatar masa cewa zuwa yanzu an kashe mutum 81 ne sannan haryanzu wasu ba su ga ‘yan uwan su ba.

” Da maharan suka diran mana, sai suka tara mu wuri daya suka ce sun zo ne su yi mana wa’azi. Suka umarce mu da idan muna da makamai mu mika su tunda wuri mu zauna mu saurari wa’azi.

” Wasun mu sun mika bindigogin su kirara adaka da addunan su. Daga nan bayan sun tattar su sai suka ja gefe suka fara bude wuta babu kakkautawa. Wasun mu suka arce da gudu wasu na faduwa wasu kuma dalma na ratsasu. Sai da suka kwashi awa shida suna abinda suka dama sannan suka gama gaban su. Sun sace shanu sama da 400 sannan kuma suka kashe duk wani makiyayi.

A karshe gwamna Zulum ya yi kira ga dakarun Najeriya su matsa domin gamawa da wadannan ‘yan ta’adda da suka addabi mutane a jihar.

Karanta labarin mu na baya:

Mummunan tashin hankali ya faru a rugar Zuwo, cikin Karamar Hukumar Gubio a Jihar Barno.

Da rana tsaka ne a ranar Talata Boko Haram suka far wa makiyayan da ke rugar Zuwo takakkiya suka yi musu mummunan kisan da suka shafe mazan kauyen baki dayan su.

Wani dan sintiri ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Boko Haram sun yi wa makiyaya maza da kananan yara kisan-kiyashi misalin 12 na rana, a inda suke taruwa su na kai shanun su su sha ruwa.

Mala Buni ya ce da idon sa ya gani, kuma ya kirga gawarwaki 69 ta mazaje da kuma kananan yara.

Sannan kuma ya ce akalla an arce da shanu sun fi 1,200. Kuma an kashe shanu za su kai 100.

“Wato harin kamar ramuwar gayya ce Boko Haram suka koma suka yi a cikin rugagen. Sun taba kai hari watanni biyu da suka gabata, amma makiyayan suka yi galaba a kan su, har aka kashe Boko Haram biyu.

Majiya ta shaida wa Premium Times cewa ‘yan Boko Haram sun sha kai samame a rugagen su na dora musu harajin-tilas. Wanda ya kasa biya sai a yi awon-gaba da dabbar sa.

“To da abin ya ishe su, sai suka fara nuna tirjiya har su na korar Boko Haram din.” Inji Mala.

Yadda Aka Yi Wa Makiyaya 69 Kisan-kiyashi:

“Akwai wata mashayar ruwa da gwamnati ta gina rijiyoyin burtsate domin shayar da dabbobin makiyaya.

“To a mashayar ruwa din ce Boko Haram suka ritsa makiyayan manya da kanana. Sun je cikin motar daukar sojoji budaddiyya har guda uku.

“Da suka fara bude wuta, makiyayan sun ja daga, amma da ya ke shammatar su aka yi, sai suka labewa jikin shanun su.

“Su kuma Boko Haram sai suka rika bude wuta kawai a kan shanun da masu boyewa a bayan shanun.

“An kashe mutum 69, Kuma an kashe shanu za su kai 100.” Cewar majiyar PREMIUM TIMES.

Bayan awa daya da faruwar lamarin, sojoji sun rika shawagi bisa jirgin yaki a wurin, amma dai ba su bi Boko Haram da harbi ba, duk kuwa da cewa ba su fi awa daya da barin wurin ba.

An ce sun sake komawa kauyen da yamma, suka kashe mutum daya da ya rage, wanda da farko ya tsere daga wurin kisan kiyashin a kan doki.

Bayan sun kashe shi, sun banka wa kauyen wuta kurmus.

Lokacin da ake rubuta wannan labarin ma kauyen na cin wuta.

Majiya ta ce tuni Gwamna Zulum ya garzaya kauyen.

Share.

game da Author