Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya fusata game da yadda manyan hafsoshin tsaron najeriya ke tunkarar yaki da ‘yan ta’adda a kasar nan, yana mai cewa abinda suke yi bai taka kara ya karya ba ganin yadda ta’addanci ke kara samun gindin zama a kasar nan.
Mai ba shugaban kasa Shawara kan harkar tsaron kasar nan, Babagana Mongonu ya shaida wa manema Labarai a fadar gwamnati cewa shugaba Buhari ya ce ba zai sake sauraran su ba idan suka zo masa da wani abu ba nasara ba.
Ya gargade su da su maida hankali su je su yi aiki tukuru ko kuma ya dau mataki akan su.
Buhari yayi ganawa ta musamman da manyan hafsoshin tsaron kasar nan a fadar shugaban Kasa, ranar Alhamis.
Wannan ganawa ya zo ne bayan kasar Amurka ta soki Najeriya kan yadda ‘yan ta’adda suke kashe mutane a yankin Arewacin Najeriya babu kakkautawa, cewa lallai gwamnati ta karkato da akalar ta zuwa ga samar wa mutanen kasar tsaro yadda ya kamata.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIME ta kawo rahoton yadda akalla mutum 14 suka rasa rayukan su a Najeriya cikin mako daya a dalilin hare-haren ‘yan ta’adda musamman a yankin Arewacin Najeriya.
Mahara musamman a yankin Arewacin Najeriya na cin Karen su ba babbaka, a jihar Katsina, Kaduna, Zamfara da Sokoto mutane na fama da hare-haren yan’tadda. Da yawa daga cikin mazauna kauyuka sun yi hijira zuwa birane domin tsoron diran mahara.
Discussion about this post