BUDE WURAREN IBADA A ABUJA: Dokoki 27 da masallatai da Coci za su kiyaye – Ministan Abuja

0

Sakamakon ganawar da ministan Abuja Mohammed Bello yayi da shugabannin addini domin samun matsaya akan sake bude masallatai da coci don ci gaba da ibada, an tsara dokokin da za abi domin kiyaye wa da kauce wa daga kamuwa da COVID-19.

Ga dokokin:

1 – A tabbata an wadatar da sabulu da ruwa a koda yause domin wanke hannaye da kuma man tsaftace hannaye a kofofin shiga masallaci ko coci, har da wuraren yin tsarki da wanka.

2 – Duk wanda ya zo masallaci ko coci sai ya tsaftace hannayen sa kafin ya shiga.

3 – A samar da na’urar gwada yanayin zafin jikin mutum

4 – Tilas masallaci, da wanda ya halarci coci ya saka takunkumin fuska.

5 – A nisanta kai daga yin musabaha da hannu, rungume juna, Sumbatar bake, raba takardun sakonni, yin amfani da dadduma ko tabarma tare da wani ko wasu, lasifika da sauransu.

6 – Masallatai da coci a Abuja za su rage yawan mutane domin a samu iya tabbatar da tazarar akalla mita 2 a tsakanin mutane.

7 – An hori shugabannin addini su nade dadduman dake cikin wuraren ibada domin samun tazarar da mutane zasu ba juna, sannan wadanda suke daga wuri daya su kebe a wuri dabam.

8 – A rage yawan masu aikin sa kai a wuraren ibada. Idan mutum ya zarce shekara 55, ya hakura da aikin.

9 – Dole shugabannin wuraren ibada, wato masallatai da Coci su sa ido wajen ganin mabiya sun bi dokokin da aka shimfida.

10 – Coci-coci za su rika budewa daga karfe 5 na safe sannan su rufe da karfe 8 na dare. Kuma kada a wuce awa 1 a tsakanin wani sashen. Za a rika hutawa na minti 30.

11 – Masallatai za su rika budewa minti 15 kafin a kira sallah, sannan kuma kada a wuce minti 10 bayan anyi sallah. Kuma a rage tsawon salloli domin rage gwamatsuwa.

12 – A ranakun Juma’a kuma, za a rika bude masallatai minti 20 kafin sallah, a kuma rufe masallatan minti 20 bayan an idar da sallah. Kada sallah da khuduba ya wuce awa daya cif.

13 – Makarantun Islamiyya, yin kiyamul lallai da ake yi a coci, makarantun lahadi-lahadi na yara duk za su ci gaba da zama a garkame. Salloli biyar da Juma’ a ne kawai gwamnati ta amince a yi su.

14 – Tarukan da zai sa a gagara samun tazara a tsakanin mabiya bai halatta ba. A yi amfani da wani hanya don sadar da sako.

15 – Masallatai da Coci-coci su tabbata an samar da kofofin shiga da na fita dabam.

16 – Ba a yarda a zauna a masallatai ko Coci bayan an idar da ibada ba.

17 – Wuraren kasuwanci da ake hada-hada a haraban masallatai da coci-cocin za su ci gaba da zama a kulle.

18 – Duk wadanda shekarun su yayi nisa, ko kuma yake fama da rashin lafiya kamar, Kanjamau, Ciwon siga, Hawan jini da sauran su ya yi sallar sa agida kawai.

19 – Ana kira ga masallatai da coci-coci su cire daddumar kasa sannan kuma a rika yi wa wuraren ibada feshi.

20 – A rika bubbude tagogi a lokaci ake cikin masallaci ko coci saboda iska ya rika ratsawa.

21 – A rika wanke wuraren da akwai cunkoso da wuraren wanka da wuraren da jama ke taruwa sannan a rika yin feshi akai-akai.

22 – A rika tunasar da mutane game da yadda ake kamuwa da cutar da hanyoyin da za a rika kiyaye wa don kauce wa kamuwa da ita.

23 – Duk wanda yake jin rashin lafiya musamman idan yayi kama da na cutar COVID-19 kamar, Zazzabi, Tari, katsewar numfashi ko kuma an yi mua’amula da wanda ya kamu da cutar, shima ya dakata a gida ya killace kai.

24 – Duk wanda aka samu yanayin jikin sa yayi zafi kada a barshi ya shiga wurin da jama’ a suke a masallaci ko coci.

25 – A rika daukan bayanan masu halartar masallaci ko coci domin a iya gano inda mutum yake zaune idan har ana bukatar haka.

26 – A kaurace wa yin taron ibada a gidaje.

27 – A karshe, Minista Bello ya ce har yanzu ana samun karin mutane da yawa da suka kamu da cutar a Abuja, saboda haka yana kira da kuma rokon mutane su maida hankali wajen kiyaye kan su, da kauce wa duk abinda zai sa su kamu da cutar.

Share.

game da Author